Adthis

Yadda Zaka Goge Bashin Dakaci A Kowani Layin MTN Batareda Kosisin Ka Ba

Saturday, 6 April 2019

Yadda zaka samu Maki 280 a jambAssalamu Alaikum, wadannan shawarwarine da babu shakka idan dalibi ya bisu sau da kafa to Insha Allahu zai samu gagarumin maki a jarabawarsa ta Jamb.

Kamar yadda dalibai suka sani an fara fitar da slip na jamb wato takardar dake dauke da rana da wurin yin jarabawar, wadannan shawarwarin za su taimaka matukar wajen samun gagarumar nasara


1. Ka tabbatar ka karanta littafin da Jamb suke bayarwa sosai da sosai, inda baka gane ba kayi tambaya, kada ka tsallake wuri wai don baka sani ba.
2. Ka tabbatar kayi Register akan lokaci, wannan zai baka dama kayi jarabawarka akan lokaci, sannan wajen register kayi nazari sosai kar ka cike ko aciki maka abinda bashi kake bukata ba.
3. Ka duba syllabus da suka baku na wuraren da za’a yi muku tambayoyi akai ka tabbatar ka bibiyesu sosai da sosai.
4. Ka tsara time table din karatu lokaci kaza zaka yi kaza lokaci kaza zaka yi kaza.
5. Ka tabbatar kana da sanayya akan computer musamman bangaren yadda ake zana jarabawa, idan baka sani ba ka nemi littafi na mai suna “Takardar Sanin Makama Ga Daliban Da Zasu Zana Jarabawar Jamb”

Friday, 15 March 2019

Dalilan Da Suke Sa Yan Matan Jami'a Wahalar Samun Mazan Aure1) Ta samu gurbin ci gaba da karatu a wata jamia, mahaifanta
sun yarda da ita da tarbiyyar da suka ba ta sai suka amince ta
tafi saboda abun da ta ke so kenan ci gaba da karatu. Saurayin
da yake son ta shi ma ya ce ba komai zai jira ta.
2) Da ta tsinci kan ta a bakon muhallin da take ta muradin
zuwa, ta hadu da sabbin mutane amma dai wadanda suka fi
jan hankalinta sune irin wadanda ake kira da manyan yara,
masu kai da gashi a cukurkude kamar shekar ungulu da sa
wanduna masu zama a rabin mazaunai kamar suna jin kashi,
ga mota kuma duk wayoyinsu iPhone ne latest. Ita ma saboda
kyan ta kuma saboda su mayun fararen mata ne ta ja
hankalinsu.
3) Lokaci ya tafi a yayin da alakarta da manyan yara ta fara
nisa, suna kashe mata kudi fiye da yadda ake ba ta a gidansu,
a hankali sai ta yi watsi da wannan yardar ta mahaifanta, ta
watsar da komai a yayin da yaudarar manyan yara ta rinjaye ta
ta fara baza musu kafa.
4) Saurayinta na gida ya fara korafin ta daina daga wayarsa,
abun da bai sani ba shine saboda yanzu tana rayuwa da
manyan yara masu gashi ta fara ganinsa wani local, da wani
sunansa Garba kamar garmar noma da kansa marar gashi
kamar kabewa. Daga baya dai ya ga ba zai iya jura ba, ita ma
kuma ta sanar masa ya hakura da ita ya nemi wata a
makwabta daidai shi.
5) Lokaci yana ta tafiya har an yi shekara guda an dauki sabbin
dalibai, shekar manyan yara ta fara tashi daga kan ta zuwa kan
sabbin dauka, ta neme su a waya da kuma a aji amma sun ki
saurararta.
6) Da daddare ta kasa barci saboda tunane-tunane, ta janyo
wayarta ta shigo facebook akalla ko za ta ga wani abu da zai
debe mata kewa amma ba ta gani ba sai wanda yake shirin
rusa mata kwakwalwa, saurayinta da ya ce zai jira ta ita kuma
ta ce ya bar ta, ya bar ta din da dadewa kuma gashi yanzu ya
dora katin daurin aurensa. Ta ji kamar duniyarta an dawo da ita
sama na kallon kasa.
7) Ta kashe duk kudadadenta kuma in ta nema a gida sai ta yi
awanni na bayanin abun da ta yi da su kafin ta samu wani,
manyan yara sun koma da shekarsu kan wasu, abincinta ya
kare. Tana ta tunanin neman mafita kafin a karshe ta yanke
shawarar ta kira tsohon saurayinta.
8) Ta kira shi ta ba shi hakuri, ya sanar mata komai ya wuce
amma dai lokaci ya kure. Ta nemi ya taimaka ya ara mata kudi
ko 3K ne, ya ce ba komai zai turo mata 5K kyauta, kuma bai
kullace ta ba , za ma su iya zama abokai.
9) Ta yi kuka kamar ba gobe musamman ma lokacin da ta hau
whatsApp ta duba status ta ga tsohon saurayinta ya dora
hotonsa da wacce zai aura, ta ji kamar ta tura masa da emoji
na miciji saboda tsabar yadda ta ji ta tsane ta, amma dai ba ta
yi ba.
10) Bayan kwanaki da aladarta ta yi latti da kwana hudu da
wasu bakin alamu, hankalinta ba karamin tashi ya yi ba, ta
yanke shawarar ta yi pregnancy test. Ta siyo kit din, ta zo ta
shirya komai ta tsaya tana kallon kit din a cikin tsananin
damwua tana adduar kar layuka biyu su bayyana.
A karshe layuka biyun sun bayyana, ya bayyana tana da ciki. Ta
yi nadama matsananciya, ta butulcewa yardar mahaifanta a
kanta, ta bi son zuciyarta. Ta yi ihu, ta cukurkuda gashin kanta,
ta daki gado kafin ta ji kamar ta kashe kanta.
Amma kuma kashe kai baya maganin damuwa ko ciwo, hasali
ma dai damuwar ake rabawa dangi da masoya muddin rai!
Abubakar Auyo

Monday, 28 January 2019

Aure Bautar Ubangiji

AURE BAUTAR UBANGIJI
=
Wannan shine bayani na shida:

_Bayan haka in ba'a mantaba har yanzu dai muna cigaba da bayanin irin mazajene wadanda sukafi alheri wadanda sukafi cancanta abasu aure****_
      _Abaya munji labarin Auren julaibib dakuma albarkarda matar tasamu da ribarda taci na aurenshi duk da cewa bashida ko sisi be ajje ba beba kowa ajiya ba kuma gashi mummuna amma kunji dai irin alherinda yabiyo baya wanda hatta iyayen nata su kansu sunyi alfahari da wannan aure sunji dadinshi har suka koma ga Allah suna farin cikin wannan aure,****_
        _To amma yanzu a wannan zamanin semuka juyarda abin muka zama babu ruwanmu da bin waccan wasiyyar ta manzon Allah, takaimu ga yau iyaye har bin bokaye sukeyi akan sunaso wai ajuyo musu hankalin wani dan yazo yanemi 'yarsu dan su samu damarda zasu tatsi dukiya ajikin wancan mutumin***_
         _Yau takaimu ga har abun yazama gasa akeyi wajen cewa anaso 'yata dole seta auri mijinda zata kece raini wanda ze siya mata mota yasiyawa iyayenta gida koda kuwa wannan dukiyar tashi bata halas bace****_
         _Iyaye a yau babu ruwansu kawai duniya suke dubawa yaki halas yaki haram sudai kawai burinsu shine wai sukai 'yarsu inda zasu huta, can kenan abakinsu suke fadar haka****_
    _To wannan irin qazamin ra'ayin namu damuka riqe a yau na cewa bazamu bayarda aure ba se ga wanda yake da dukiya dan kawai musamu duniya, amma idan mutumin kirki me addini yafito neman auren 'yarmu to lallai Annabi (s.a.w) yace mubashi aure, inkuwa muka hana to 6arna zata yadu abayan qasa da fitina, wanda kuma gatanan yanzu haka muna gani, fitinar yau daban ta gobe daban, wanima idan ka aura masa 'yar taka seya maida ita tamkar baiwa kodai yayita jibgarta kokuma yariqa zaginka agabanta kokuka yadinga daura mata hidimarda yasan cewa tafi qarfinta, hakanan ze dage yayita bautarda ita, kuma babu ruwanshi da biyan buqatunta ta kowanne bangare*****_
       _Wani zaka ganshi a waje akwai walwala ga kyauta iri iri dan neman suna, yau kajishi ance ya kashe wasu maqudan kudi can, gobe kajishi yakai kudi can, yau kaji yasaima wane mota gobe ace ya siyama wane gida, hakanan zakaji yanata faman rarraba kyaututtuka, amma itako wannan matar tashi idan kaji irin halinda take ciki na qunci da yunwa zakayi mamaki, amma wannan matsalar ba lokacinta bane yanzu dan haka zamu jingineta se can gaba idan mukazo shafinta****_
=
_Wannan fitintunu da Annabi (s.a.w) yake cewa zasu watsu abayan qasa idan ana hana irin wadannan mazaje aure, to daga cikin fitintunun fa akwai wadda ake samun kangara tsakanin iyaye da 'ya'yansu kaga ansamu takun saqa, saboda ita dai 'yar mafi yawa tasani cewa bawai son Allah da manzonshi bane yasa iyayenta suka qi amincewa ta auri wannan bawan Allah wanda ita tana kyautatamasa zaton cewa mutumin kirkine, kawai wani kwadayin duniya shine yasa sukaqi yarje masa subashi aurenta kokuma wani ra'ayi nasu na can daban, amma mafi yawa idan kaga ansamu irin wannan matsalar to zakaga iyayen mafi yawa ba saboda Allah da manzonshi suke qoqarin hanata wanda takeso ba saboda wata manuface tasu****_
      _To daga wannan lokacinda wadannan iyayen sukayi hakan to shikenanfa sun qunsa bakin ciki a zuciyar wannan 'ya tasu, sekaga wata dalilin haka ta fada ga zinace zinace, wata sekaga ta kangarema iyayen bata musu biyayya kokuma ta auka ma shan miyagun qwayoyi kokuma ta auka cikin wannan bala'in na madigo wanda yazama fitina ga musulmai ahalin yanzu****_
          _To lallai 'yan uwa daga cikin hanyoyinda zamubi mu yaqi matsalar zinace zinace da madigo acikin wannan al'umar tamu, shine aduk sadda mutumin kirki bawan Allah me addini da kyawawan dabi'u yafito neman auren 'yarmu to lallai mubashi kada tunanin wani abin duniya wanda ba me dorewa ba, yasa muhanashi bayan kuma shi yanason yarinyar itama tana sonshi****_
=
=
Zamu dakata anan sekuma bayani nagaba idan Allah yakaimu
=
_Almajirinku ne kamar kullun, dan mutanen Kabo_
.
```Jameel Alhassan Haruna kabo```
.
_(Alwahhaby, Assalafy)_
.
.
Allah ta,ala yasa mudace.mahuta.com.ng

Tuesday, 15 January 2019

Yadda Zaka Nemi Aikin Zabe(Ad-hoc Staff)

Yadda Zaka Nemi Aikin Zabe Na 2019.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta saki form na neman aikin zaben shekara 2019.

Neman aikin yakasu zuwa biyu:
• Ma’aikatan wucin Gadi (Adhoc Staff – RATECH)
• Ma’aikatan INEC na dindin din (LGATECH)

Ana iya rijistar wannan ayyuka guda biyu a shafin INEC na yanar gizo wato pres.inecnigeria.org Sai dai kuma ba kowa zai ci gajiyar aikin ba, har sai mutun ya cika ka’idojin da sashen fasaha na hukumar zaben ya gindaya.

Sharudan Rijista Dan Zama Adhoc Staff – RATECH
Mutane Kala uku ne za su iya rijistar wannan aikin.
1. Wanda ya yi bautar kasa da hukumar INEC tsakanin 2013 zuwa 2018 (Ex-coper)
2. Ma’aikacin hukumar INEC mai Karamar diploma zuwa sama. Ya zamana yana da ilimin na’ura mai kwaqwalwa.
3. Dalibin jami’ar tarayya ko kwaleji ko poly wanda saura shekara daya ya gama karatu. Shi ma sai yana da ilimin na’ura mai kwakwalwa.

Abubuwan Da zaka tanada
• Dole ne ya zama kana da lambar waya da kuma email address
• Referral letter daga ma’aikacin gwamnati da ya taka matsayin aiki na GL14 zuwa sama.
• Hoton ID card.

Sharudan Rijista Dan Zama INEC Staff – LGATECH
• Iya ma’aikacin INEC mai ordinary national diploma zuwa sama zai iya register. Shi ma sai yana da ilimin na’ura mai kwakwalwa.
• Dole ne ya zama kana da lambar waya da kuma email address
• Hoton ID card.

Sunday, 13 January 2019

An Kama Masu Daukar Nauyin Yan Ta'adda a Jihar Zamfara

 1. ANKAMA MAYAN 'YAN KASUWAR DAKE DAUKAR NAUYIN 'YAN BINDIGAR ZAMFARA A JAHAR

  - 'Yan sanda sun kama wasu mahauta 'yan asalin jihar Zamfara mazauna Legas bisa zarginsu da daukan nauyin 'yan bindigar Zamfara
  - Mahautan guda hudu da aka kama sune Alhaji Ago Atine, Alawani Abubakar, Mohammad Sahagari da Bashir Aliyu
  - Alhaji Altine ya ce wani Alhaji Naira ne ke sayar masa da shanun da araha shi kuma ya sayar da su da tsada a Legas
  - Sashin tattara bayanan sirri na 'yan sanda ya gano cewar 'yan bindigan na amfani da kudin da suke samu daga sayar da shanun satar ne wurin sayo makamai

  Rundunar 'yan sandan Najeriya ta kama wasu mahauta hudu da ke sayar da nama a Agege na jihar Legas bisa zarginsa da daukan nauyin 'yan bindiga da ke kai hare-hare a wasu garuruwa a jihar Zamfara.

  The Punch ta ruwaito cewa garuruwan da aka kai harin sun hada da kananan hukumomin Tsafe, Zurmi, Shinkafi Maradun, Mari da Birnin Magaji.
  'Yan sandan sunyi ikirarin wadanda ake zargin su ke samarwa 'yan bindigan kudaden da sukae sayan makamai ta hanyar sayan shanun sata daga hannunsu. Wadanda ake zargin sune Alhaji Ago Atine, Alawani Abubakar, Mohammad Sahagari da Bashir Aliyu.

  An gano cewar 'yan bindigan da suka kashe mutane da dama sunyi amfani da kudin da suka samu bayan sayar da shanun ne wajen sayo bindigu da wasu muggan makamai daga kasar Libya.
  Majiyar Legit.ng ta gano cewa sashin tattara bayyanan sirri na 'yan sandan Najeriya sun damke kwamandan 'yan bindigan ne a Zurmi kuma ya tona yadda 'yan bindigan ke samun kudin sayan makamai.

  An kama wadanda ake zargin su hudu ne yayin da suke kokarin sayar da wasu daga cikin shanun satar ga wani mutum.
  Daya daga cikin wanda ake zargin, Alhaji Altine ya shaidawa City Round cewa ya saya shanu fiye da 400 daga wani Alhaji Naira. Sai dai ya ce bai san cewa shanun sata bane.

  Ya ce, "Alhaji Naira ya aiko min da shanu fiye da 400 ni kuma na sayar masa a mayanka. Na tura kudin zuwa asusun ajiyar bankin Alhaji Naira. Na saya shanun da araha, ya sayar min da kowanne guda a kan N60,000 zuwa N70,000 ni kuma na sayar da kowanne a kan N170,000 zuwa N180,000. Ban san abinda Alhaji ya ke yi da kudin ba kuma ban san shanun 

Thursday, 10 January 2019

Yadda Za Kai Rijistar Jamb Cikin Sauki


kamar yanda koya ya sani yau ne ranar da hukumar jarabawar shiga jami'a wato Jamb suka fitar a matsayin ranar fara registration na wannan shekarar.. 


After successful payment & obtaining the JAMB ePIN, the candidate would proceed to any of the accredited CBT Centres to complete his/her own registration . Remember, at this point, the ePIN would have been delivered electronically to candidates and not to be handwritten. It would be delivered directly to the phone number used to create your profile code.

At the CBT Centre, The candidate presents the ePIN at any JAMB accredited CBT Centre for validation and completion of registration for 2019 UTME. Candidate is expected to pay NOT more than N700.00 as Service Charge to the CBT Centre.

Once payment has been made to the CBT Centre, candidate Provides:

(i) Biodata: Date of Birth, Nationality, LG/State of origin, Gender, e-mail address, telephone

(ii) Choice of institutions & programmes (Disciplines)

(iii) Qualification with grades/dates, if not Awaiting Result

(iv) UTME subjects & Choice of Examination town for

(a) Mock examination (optional)

(b) Examination for UTME (actual examination)

A proper template that you can fill with parents & guardians, before heading to the CBT Centre, will be provided to you tomorrow, so ensure you check back on Myschool website to download it for free.

Before proceeding to the CBT Centre to register, candidates are advised to use the 2019 JAMB Brochure , to confirm the courses they intend to study, requirements and schools that offer such courses, to avoid time wasting.

Above all, get the 2019 JAMB CBT Practice Software or the 2019 Myschool JAMB CBT Practice App . These will enable you to cover all JAMB past questions as well as get familiar with the JAMB CBT environment before the exam.

Please note that while at the CBT Centre, you would be required to;

Do picture capture (no scanning of passport photography)

Do Biometric enrollment (10 fingers)

Review entries & confirm correctness

Print Registration Slip only by USING BIOMETRIC AUTHENTICATION to confirm valid finger-print (UTME+DE)

Collect reading text & CD

THERE WILL BE NO OFFLINE REGISTRATION, as all accredited CBT Centres have been empowered for real time online registration

Please note that you would be able to Upload of O’ level and A’ level results at the CBT Centre. This will be done by the candidate at the JAMB Portal.

Schools, Institutions, Tutorial Centres, Business Centres & Cafes can equally act as JAMB CBT Agents and Training Centres to help train students for the upcoming exams.

Tuesday, 8 January 2019

Abinda INEC Za Ta Biya Maaikatan Zabe (Ad-hoc Staff)

Kamar yadda ta saba a lokacin zaɓe. Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC), a wannan Karon ma, za tayi anfani da yan bautar kasa (Copers), da kuma ɗaliban Jami'o-in Gwamnatin Tarayya, a matsayin jami'an zaɓe, domin gudanar da zaɓen shekara ta 2019. 

Hukumar ta bayyana cewa, kaso Arba'in na wanda za su gudanar da zaɓen yan bautar kasa ne (Copers). Inda ta ke da mazaɓa 119,809 kuma akwai yiwuwar za ta kir kiri mazaɓa 30,000. 

Ga abin da za ta ba kowana jam'i. 


Yadda zaka samu Maki 280 a jamb

Assalamu Alaikum, wadannan shawarwarine da babu shakka idan dalibi ya bisu sau da kafa to Insha Allahu zai samu gagarumin maki a jaraba...