Adthis

Yadda Zaka Goge Bashin Dakaci A Kowani Layin MTN Batareda Kosisin Ka Ba

Friday, 28 December 2018

Gwamnatin Tarayya Za ta Tura Karin Jami'an Tsaro Zuwa Jihar Zamfara

Ministan harkokin cikin gida, Abdulrahman Bello Dambazau ya ce za a kara tura karin jami’an tsaro jihar Zamfara domin kawo karshen kashe-kashen da kuma lalata dukiya da ake .

Dambazau ya bayyana haka ne lokacin da ya ziyarci jihar a ranar Alhamis.

Ministan ya samu tarba daga mai rikon muƙamin gwamnan jihar, Sunusi Rikiji da kuma sauran yan majalisar zartarwar jihar.

Ya yin ziyarar ministan ya bayyana damuwar shugaban kasa Muhammad Buhari kan halayyar kin tuba da masu aikata kashe-kashe a jihar suke da ita.

“Mun himmatu wajen aiki tare da gwamnatin jiha wajen kara tura jami’an tsaro zuwa jihar,”

A ranar Laraba ne dai ministan ya bayyana cewa rikicin na Zamfara na zai iya kawo karancin abinci a kasarnan.

An Bankado Ma'aikatan Bogi Kusan Dubu Hamsin A Nijeriya

Yadda Aka Bankado Ghost Workers Dubu Hamsin A Nigeria

Menene Ghost Workers?
Sune ma'aikacin da yake karbar albashi sama da guda daya, a shekarun baya a Nigeria misali mutum yana aiki a hukumar zabe to sai yaje wata hukumar ya nemi aiki kuma a bashi, baya zuwa amma ana biyansa wannan albashin sai ka samu mutum daya da albashin mutum uku, ya toshe gurinsu.

Idan albashinka na ma'aikatar farko da kake kake aiki ya fito daga TSA Asusun Bai Daya na Gwamnatin Tarayya zuwa bankin ka sai Remita tayi copy din BVN dinka ta turawa gwamantin tarayya haka in na wata ma'aikatar yazo sai remita ta turawa gwamantin tarayya cewa wane-wane ma'aikaci a hukuma kaza ya karbi albashi sau kaza.

Da aka tsananta bincike sai da aka gano mutane Dubu Hamsin (50,000) masu irin wannan halaryar cikin ma'aikatan gwamnatin tarayya.

Sai aka dakatar duk wanda aka samu da wannan laifin ya zama albashi daya zai dinga karba, hakan yasa gwamantin tarayya ta samu rara har sama da Naira Biliyan Dari Biyu N200,000,000,000.

Acikin wannan kudinne kwanaki gwamnatin tarayya ta debi 'yan sanda Dubu Goma (10,000) ake biyansu albashi, ba wai wasu kudin albashinsu ne gwamnatin ta sake fitarwa ba.

To wannan shine yadda aka bankado Ghost Workers.

Basheer Sharfadi

Wednesday, 26 December 2018

Matar Da Tayi Yunkurin Kashe Mijinta Ta Sace Kayan Lefen Amarya

Matar nan mai suna Rabi’a Usman Muhammad KK, wacce a ke yiwa lakabi da Mami, ta sadada gidan tsohon mijinta, Nasir Sa’ad, a Kano ta sace kayan lefen da ya tanada ga amaryar da zai auro.

Rabi’a ta aikata hakan ne tare da hadin gwiwar wata yayarta da ’yar babbar yayarta da kuma wasu mutane wadanda dukkansu a nan gaba majiyar jami’an tsaro ta ce za a bayyana sunayensu a caji ofis din ’yan sandan da a ka riga a ka shigar da korafi ko kuma a kotun da za a gudanar da shari’a kan zargin sace kayan.

Lauyan tsohon mijin, Barista Nazir Adamu, wanda ya tabbatar wa da wakilinmu tuni an shigar da korafin a cafi ofis da ke GRA na Dorayi Babba Cikin Gari, ya kara da cewa, a na zargin Rabi’a tare da na hannun damanta da yin gaban kansu ne a ranar 27 ga Maris, 2018 ne, inda su ka durfafi gidan tsohon mijin da sunan za ta kwashi kayanta, duk da cewa ta san ba ya gari kasancewarsa ma’aikaci a babban birnin tarayya Abuja, amma su ka yiwa muhimman kayansa wawaso.

A cikin kayayyakin da a ke zargin Rabi’a da kwashewa akwai kwamfuta, wacce a ka kiyasta kayan da ke cikinta sun kai darajar Naira miliyan 40. Bugu da kari, an shaidawa jami’an tsaron cewa, a cikin kayan lefen akwai shaddojin Gazna da atamfofi Sufa Holan, sannan akwai kananan kayayya da su ka kwashe wadanda iyayenta ba su kawo ta gidan da su ba, kamar tukunyar gas, na’urorin dumama daki, kafet-kafet da sauransu. Hatta kayan abinci da sabulai da kayan shayi sai da su ka kwashe.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar 26 ga Maris ne Alkali Ibrahim Sarki Yola ya kashe auren, inda ya turasasa wa matar da ta biya mijin diyya bayan da lauyansa ya sanar da kotun yadda Rabi’a ta yi yunkurin kashe shi a lokacin da su ke tare, saboda ta gano ya na kokarin zai yi ma ta kishiya.

An Tura Wani Lauya Da Aka Kama Da Yi Ma Wata Yarinya Fyade Gidan Kaso

Wata babbar kotun majistri a garin Fatakwal ta bada umarnin garkame wani lauya mai shekaru 46, Kingsley Phillips a gidan Kurkuku bisa tuhumarsa da aka yi da yi ma karamar yarinya fyade.


A zaman kotun na ranar Laraba 14 ga watan Maris, kamfanin dillancin labaru NAN, ta ruwaito Alkalin Kotun, Kariba Braide ta bayyana cewa a baya tayi amfani da damarta wajen bada belin wanda ake tuhuma, ko za’a samu sulhun tsakaninsa da masu kararsa.

Tunda dai an kasa samun sulhu a tsakanin masu kara da wanda ake kara, ya zama wajibi doka tayi aikinta yadda ya kamata, don haka na janye umarnin belin, ya zama dole a garkame min wanda ake kara a gidan Yaro.” Inji Alkalin.

Majiyar ta ruwaito Alkalin Kariba tana cewa ba za tayi sakacin rabuwa da aikinta ba akan mai laifi, duk da cewa ta bashi kwanaki 16 ya sulhunta da masu kararsa amma ya kasa, hakan ta sanya babban Alkalin jihar kiranta a waya yana gargadinta akan ta yi adalci a shari’ar.

Sai dai duk magiyar da lauyoyi abokan aikin Phillip suka yi na ganin an sun samar masa beli daga kotun ya ci tura, sakamakon Alkalin ta dage kai da fata. Rahotanni sun tabbatar da cewar Philip na iya fuskantar hukuncin daurin rai da rai idan Kotu ta tabbatar da laifin da ake tuhumarsa akai.

Amfani Goma (10) Na Ganyen Gwaba

Ganyen gwaba na da matukar amfani ga lafiya

Ganyen Gwaiba ya kunshi sunadai da suka hadar da; antioxidants, antibacterial da anti-inflammatory irin su polyphenols, carotenoids, flavonoids da kuma tannins dake da matukar tasiri wajen kawar da wasu cututtuka da dama.

Tasirai da wannan sunadarai suka kunsa tare da rawar da suke takawa wajen kiwatar lafiya sun hadar da;

1. Rage nauyin jiki

2. Tasiri ga cutar ciwon suga

3. Rage teba da daskararren maiko

4. Kariyar amai da gudawa

5. Hana kamuwa da cutar nan ta hunhu wato Bronchitis

6. Waraka ga cututtukan hakori, makoshi da kuma dadashi.

7. Ciwon daji wato Kansa

8. Habaka samar da ruwan maniyyi

9. Warkar da gulando.

10. Kawar da cutar fata musamman kyazbi.

 

Ko Kasan Jami'o'in Dake Saida Takardar Digiri Dan kwatano??

Birnin Kwatano da ke kasar Benin makwabciyar Nijeriya ya shahara wajen karbar tarkace da tsofaffin kayayyakin da turawa suka gaji da aiki da su. Daga nan ake lodi a aika su zuwa kasashen Afrika.


Nijeriya ita ce hamshakiya wajen karbar gwanjon nan, domin suna da araha kuma wasu har sun fi sababbin kayan da ake kerawa cikin ha'inci karko da nagarta.
Wadannan tarkacen kayayyakin sun hada da motoci da karafuna da kayan lantarki da tsofaffin tufafi da sauran abubuwan amfanin yau da kullum. Ashe bayan kayan amfani ma har da takardar kwalin digirin digirgir!
Ga wanda ke son samun mataki na daya akan kowanne irin karatu yake bukata cikin wata shida, zai iya shiga daya daga shagunan makarantun da ke baje ko'ina cikin Nijeriya, ya biya kudinsa nan take a ba shi takarda ba tare da ya shiga aji ko sau daya ba. Wani karin armashi ma har yana da ikon zuwa hidimar kasa.
Kodayake, tuni gwamnatin Jamhuriyar Benin da ta Nijeriya suka nisanta kansu daga irin wadannan shaguna da ke ikrarin bayar da digiri dan Kwatano, har yanzu babu wani mataki da aka dauka na dakile faruwar haka.
Kwanakin baya wata jami'a mai suna ISM Adonai ta nisanta kanta da wata makaranta dake Kano mai suna Imperial Leadership College, wadda aka ce ta karkashin ta za ka iya yin karatun digiri da jami'oi sama da guda 30. Kuma fa duka - duka ofis biyu ne da makarantar, amma a lokaci guda ana iya koyar da dalibai fiye da dari wadanda ke halartar makarantu daban-daban ciki har da daliban da ke koyon aikin likitanci da tiyata!
Da na bincika sai na samu labarin cewa, ba wannan makarantar ba ce kadai a fadin birnin Kano, akwai wata ma wadda wasu manyan malaman jami'a da ke kayar da mutane a makarantun gida, amma idan sun dawo da karatunsu wajen, sai su ba su 'First Class' cikin watanni 6 zuwa 12 kacal.
Akwai wata makarantar ma da aka ce malami daya ne yake koyar da dukkan daliban tun daga level 1 har zuwa 4, kuma kowanne dalibi da first class yake fita cikin kankanin lokaci. Ya danganta da yawan kudin da ya bayar.
Wata makarantar kuma wadda hedkwatar ke garin Ibadan da reshenta a unguwar Sabon Garin Kano, an ce shugaban makarantar takardar sakandare gare shi mai dauke da Pass 3 Credit 1. Tuni dai hukumar ICPC ta cafke shi lokacin da wani dalibinsa ya kai shi kara saboda gaza samar masa da takardun shiga NYSC da ya yi.
Zan dora a kashi na biyu.
Danladi haruna

KAYI RIGISTA YANZU - TSARIN P-YES NA GWAMNATIN TARAYYA

An samar da tsarin karkashin ofishin sakataren gwamnatin tarayya da kuma ofishin mataimaki na musamman ga shugaban kasa akan harkokin matasa da kuma dalibai.

Ana shirya tsarin domin samarwa matasa Dubu Dari Bakwai Da Saba’in Da Hudu ayyukan Yi.

*Abubuwan Da Mutum Yake Bukata Domin Neman Wannan Damar:*
1. Ya zama dan Nigeria
2. Daga dan shekaru 18 zuwa 40
3. Ya zama kana iya jin harshen turanci da kuma wani daga yaren da ake amfani dasu a Nigeria
4. Dolene ka cike form na wadanda zasu tsaya maka (Guarantor)
5. Shaidar zama dan karamar hukuma.

*Yadda Ake Neman Wannan Damar Shine”*
1. Zaka shiga shafin da aka samar domin wani yin register wannan tsari watohttp://applicant.p-yes.gov.ng/signup

2. Idan ba zaka iya cikewa ta nan ba zaka iya zuwa kafa da kafa domin karbar foam din wannan tsarin da zaka cike abubuwa direshi kamar haka:

Menene Katin Zabe? Da Yadda Ake Yinsa

Menene Katin Zabe?
Katin Zabe (Voters Card) shine katin da zai baiwa duk wani dan Nigeria mai shekaru Sha Takwas (18) zuwa sama damar kada kuri’ar sa a matakan zaben Shugaban kasa, Gwamna, ‘Yan Majalisun jiha, tarayya da Dattijai, shugaban karamar hukuma da Kansiloli.

Abubuwan Da Ake Yi Da Katin Zabe
Baya ga yin zabe kuma ana amfani da katin zabe wajen register wani abu na hukumomi, ko bankuna da sauran duk wani abu da ake yi da Valid ID Card.

Su Waye Ke Yin Katin Zabe?
Hukumar zabe ta kasa itace ke da alhakin yiwa ‘yan kasa katin zabe.

Ana Biyan Kudi Domin Yin Katin Zabe?
A’a katin zabe kyauta ne ba’a bada ko sisi duk wanda ya karbi kudinka da sunan katin zabe to ka wurgashi ga mahukunta.

Su Waye Ya Halatta Suyi Katin Zabe?
Duk wani dan Nigeria da ya kai shekara 18 zuwa sama to shine ke da ‘Yancin yin katin zabe.

Yaushe Ake Yin Katin Zabe?
Yanzu ba kamar shekarun baya ba da ba’a yin katin zabe sai lokacin da zabe ya karato a’a yanzu kowane lokaci mutum yake so zaije yayi, sai dai kawai yanzu an dakatar har sai bayan zaben 2019 za’a cigaba da yi.

Yaya Ake Yin Katin Zabe?
1. Zakaje ofishin hukumar zabe na karamar hukumar ka.
2. Zasu duba suga shekarunka sun kai? Idan basu gamsu ba musamman irina masu karamin jiki to za’a ce ka kawo Takardar Shaidar Haihuwa.
3. Za’a baka foam ko lamba.
4. Ana bin layi saboda yawan mutane (a baya).
5. Za’a shigar da bayanan ka.
6. Za’a yi maka hoto.
7. Zakayi thumb print.
8. Sai a cire maka katin zabe na wucin gadi (temporary voters card).

Yadda Zaka Karbi Katin Zabenka
Bayan ka karbi katin zabe na wucin gadi to zaka dan jira kadan, sai dai shi ba kamar katin dan kasa ba, baya jimawa sosai.
Zaka iya dubawa ta website din INEC domin ganin ko katin ka ya fito? Wani lokacin kuma suna bada sanarwa cewa daga wata kaza zuwa wata kaza wadanda sukayi katin zabe to katinsu ya fito sai kaje ka karba.

A watannin baya kadan na samu tattaunawa da Jami’in hurda da jama’a na hukumar Zabe ta Jihar Kano Malam Garba Lawal Muhammad kuma ya tabbatarmin cewa yanzu haka suna da dubunnan katinan zabe a ajiye masu shi basu zo sun karba ba.

Allah Ya Taimaka.

Basheer Sharfadi
Social Media Strategist.
December, 2018.

Batutuwan Da Majalisar Ministoci Ta Amince Dasu a Wannan Makon

A zaman majalisar ministoci na wannan mako a karkashin jagorancin Shugaba Muhammad Buhari, majalisar ta amince da Nijeriya ta  fice daga wasu kungiyoyin kasa da kasa har 90 daga cikin 310 take ciki.

Da take karin haske kan zaman majalisar, Ministar Kudi, Kemi Adeosun ta ce matakin ya zama dole saboda Nijeriya ba ta amfana daga kungiyoyin sannan wasu daga cikinsu ma, ba su da sauran tasiri a duniya. Ta kara da cewa, hakan zai sa Nijeriya ta samu rarar dala milyan 70 a kowace shekara daga kudaden da take kashewa a kan wadannan kungiyoyin.

Masu Garkuwa Da Yan Agajin Izala Sun Bukaci Miliyan 30 Kafin Su Sake Su

Masu garkuwa da mutane da suka sace ‘yan agaji 20 a hanyar komawar su gida bayan sun halarci wa’azin kasa na kungiyar Izala aka gudanar a birnin Dutse na jihar Jigawa, sun bukaci sai an ba su naira milyan talatin kafin su sako su.

‘Yan agajin sun fito ne daga karamar hukumar Sabon Birni dake jihar Sokoto. An yi garkuwa da su ne a hanyar komarwarsu gida.

Ana bukatar ‘yan al’ummar musulmai da su saka wadanan bayin Allah a cikin addu’o’i.

Dattawan Jihar Kano Sun Bukaci Yan Sanda Su Binciki Gwamna Ganduje

Kimanin makonni biyu bayan da babbar kotun Kano ta haramtawa Majalisar dokokin Jihar bincikar faifen bidiyon dake zargin gwamna Abdullahi Umar Ganduje yana karbar cin hancin dala miliyan biyar, dattawan Kano sunce akwai bukatar gwamnan ya yiwa al’umar jihar bayani da zai gamsar da su game da zargin.

Hakan dai na zuwa a dai-dai lokacin da jama’a ke korafi kan yadda dattawan na Kano suka ki cewa uffan tun bayan da Jaridar Daily Nigeria ta fara kwarmata zargin karbar rashawar akan gwamna Ganduje.

Daya daga cikin dattawan Jihar Kano, Alhaji Gidado Mukhtar, yace abu na farko da ya sa dattawan ba su yi magana ba shine domin maganar tana gaban kotu, da bisa doka bai kamata a saurara, na biyu kuma magana irin wannan idan ta taso ya mata a tsaya a ga inda ta gangara kafin aga mene ne a ciki.

Gidado yakara da cewa tunda kotu tayi hukunci ‘yan sanda suna da hakki da kuma damar su bincika wannan zargi da ake yiwa gwamna Abdullahi Umar Ganduje, yanzu suna sauraron ‘yan sanda su yi aikin daya kamata wajen bincikar wannan zargin karbar cin hancin.

Burina na saita Nijeriya Akan Tafarkin da Al'umma Za su ji Dadi - Shugaba Buhari

“Ubangiji Ya san zuciyata, ba ta da wani buri da ya wuce na sai ta kasata Nijeriya, a tafarkin da za ku ji dadi nan gaba, domin kune matasa masu tasowa.

Akwai tsananin wahala a mulki, yayin da kake koqarin kawo canji a kasa Kamar Nigeria, Zaka hadu da Kalubale Kala Kala mai Wahalar gaske.

Muna iya kokarinmu a yanzu domin mu ga komai ya daidaita a kasar mu, kuma na tabbata koda abokan hamayyar mu sunsan cewa muna iyakar kokarimu don ganin mun daura kasarmu a turbar data dace.

Amman na san wasu daga cikinsu suna ganin mun yi laifi, sakamakon hana ha’inci da almundahana da dukiyar al’umma.

Ga wadancan ‘yan siyasa, masu sha’awar abarsu suyi wadaka da kudin gwamnati mun san bazasu ta6a yafe mana ba Ko kuma su ga kokarinmu. Ba za su gani ba.

Domin ana su tunanin ba mu kyautata musu ba, mun yi musu laifi, laifin kuwa shine:-
Mun toshe musu duk wassu hanyoyin dasuke bi wajen sace dukiyar al’ummah. Dominsu
basu da wata damuwa, illa abarsu suyi badakala da dukiyar kasa.

Sun yarda da haka koda kasarnan zata lalace, domin suntara kudaden da gidaje a ketare.

Sun shirya tsaf da karfinsu domin wargaza shirin da muka soma na saita wannan kasar tamu, basu da damuwa koda da kwayar zarra, dangane da damuwar mutanen kasar nan .
Bamu da wani za6i, Illa za6in mutanan Nijeriya, idan sun amince da kokarinmu, zasu iya sake za6anmu a karo na biyu domin cigaba daga inda muka tsaya, Hakanne zai amfanemu Baki daya.

Idan kuma baku aminta damu ba, zaku iya komawa garesu ba (wato yan jari hujja ). Domin wargaza muku rayuwar ku ta nan gaba, dama kasar baki daya.

Amma na tabbata zaku tuna cewa na fada muku gaskiya ko bayan Raina, kuma nayi iya kacin kokarina domin naga kasarmu ta hau turban gaskiya, da rikon amana, Za6i ya rage naku ‘yan Nijeriya. domin kasarmu.

Allah ya san zuciyata da abinda ke cikinta, inayin wannan maganane tsakanina da Allah.

ALLAH YA TAIMAKI KASATA DA AL’UMMARMU BAKI DAYA.”

Wani uba ya kashe 'Yar cikinsa a Kano

A karamar hukumar Rimin Gado dake jihar Kano wani mutum mai suna Sani Lawan Kofar Gabas ya kashe ‘yarsa mai shekara Uku a duniya bisa ta dameshi kuka.

Kakakin rundunar ‘yan Sandan jihar Kano, SP. Magaji Musa ne ya bayyana wa manema Labaru hakan a ranar Litinin a Kano.

Majiyarmu ta ‘Kano Today’ ta ruwaito cewa mahaifin yarinyar ya yi sanadin mutuwar yarinyar ne ta bata gubar Fiya-Fiya da yayi ta sha.

Lawan Kofar Gabas ya amsa laifinsa, inda ya ce ya fusata da ita ne yayin da ta ishehsi da kuka saboda wani ciwo da ta ji a kafarta.

Kakakin ‘yan sandan jihar Kano, ya ce karamar yarinyar ta fara amai baya da aka bata gubar, inda mahaifin da kaninsa suka yi gaggawar kai ta asibiti amma daga bisa ‘yar ta mutu tun kafin likitoci su kai ga tabata.

Magaji Musa ya ce nan ba da jimawa za su mika mahaifin yarinyar ga kotu domin ya karbi hukunci daidai da abin da ya aikata.

Kakan yarinyar Malam Saminu Sulaiman wanda ya yi magana a madadin iyalan yarinyar, ya ce za su tabbatar da mahaifinta ya fuskanci hukuncin kashe ‘yarsa da ya yi.

Tuesday, 25 December 2018

Yadda zaka bude account din banki ta facebook


Cigban fasaha: Shin ko kasan zaka iya bude Bank Account ta Facebook? Author: Al’amin Jamil Musa Mai karatu barka da warhaka da fatan kana jin dadin kasancewa da mu. Kasancewar al’amarin wannan duniya ta fuskar fasaha kullum kara gaba yake. A yau mun zo muku da yadda zaka bude asusun ajiya na Banki wato Bank Account ta FaceBook, wannan fasahar da zata bawa mai amfani da shafin sada zumunta na Facebook damar bude asusun ajiya na banki cikin kasa da mintuna 5 ba tare da kaje banki ba. YADDA ZAKA BUDE ACCOUNT DIN; Nasan da daman masu amfani da Facebook messenger kan ci karo da tallan Bankin UBA wato UBA […]

Shehu Sani ga Buhari: Ka ziyarci Zamfara kafin yakin neman zabe a Akwa ibom

Shehu Sani, sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya ya yi kira ga shugaban kasa Muhammad Buhari da ya kai ziyarar ta’aziya jihar Zamfara kafin ya kaddamar da gangamin yakin neman zabensa a jihar Akwa Ibom.

Sanatan ya bayyana haka ne cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

An shirya Buhari zai kaddamar da yakin neman zabensa a Uyo babban birnin jihar Akwa Ibom ranar Juma’a.

Amma Sani ya yi kira ga shugaban kasar da ya fara kai ziyara jihar Zamfara da kashe-kashe suka yi wa katutu.

Rikici ya barke a jihar ranar Litinin bayan da wasu yan gudun hijira suka gudanar da zanga-zanga kan kashe-kashen dake faruwa a yankunsu.

Sani ya ce yana fatan shugaban kasar zai yi amfani da shawarar tasa.

Mabiya addinin shi'a sun taya kiristoci murnar kirsimeti

A lokacin bukukuwan Kirsimeti da Kiristoci ke gudanarwa a fadin duniya, ‘Yan Shi’a Almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky sun yi amfani da wannan damar wajen kaiwa Kiristoci ziyarar a cocin ECWA GOODNEWS dake Kaduna.

Shugaban Cocin Rabaran Istifanus Isa ya gabatar da wakilin ‘Yan Shi’a a wurin wato Dakta Shu’aibu Musa, inda ya yi jawabi na taya murna da kuma gabatar musu da saƙon ‘yan Shi’a, da kuma matsayin Kiristoci a wurin ‘yan Shi’a da sauransu. Bayan nan ne, aka gabatar da waƙoƙi daga Ammar Ɗan Tinka da Muhammad Baƙir.

Mahalarta Cocin, sun nuna jin dadinsu sannan sun ce; sun ƙara fahimtar Musulunci ba addinin ta’addanci bane, addini ne na zaman lafiya. Sun kuma nuna gamsuwarsu da yadda ba a kyamace su har aka zo muhallinsu domin taya su murna.

Monday, 24 December 2018

Hanyoyi 5 da zasu taimaka wajen hana kamuwa da cutar Hepatitis

Cibiyar kula da hana yaduwa da kawar da cututtuka CDC ta sanar cewa cutar Hepatitis cutace da ke kama huhun mutum kuma ya na neman ya zama ruwan dare a duniya musammman a wasu kasashen Afrika.

Hukumar ta ce cutar Hepatitis na daya daga cikin cututtukan dake kashe mutane farad daya saboda da sai cutar ta kama jikin mutum sosai sannan ake iya gane wa. Misali bincike ya nuna cewa cutar ta kashe mutane sama da miliyan 1.34 a cikin shekara daya.

Hukumar CDC ta kara da cewa yadda ake kamuwa da cutar ya danganta da irin cutar domin cutar nau’ I nau I ne da ya hada da Hepatitis A,B,C,D da E. Misali jaririn da ke cikin uwarsa zai iya kamuwa da cutar Hepatitis C, ana iya kamuwa da cutar Hepatitis A da E ta hanyar bayan gida ko kuma a ban daki mara tsafta.

Hanyoyin kamuwa da cutar ya hada da

1. Yin Jima’I batare da amfani da kororo roba ba

2. Kara jinin mai dauke da cutar.

3. Jariri na iya kamuwa da cutar Hepatitis tun a cikin uwarsa.

4. Amfani da reza,magogi, allura da wanda ke dauke da cutar.

5. Shan ruwa mara tsafta da cin wasu ganyayyakin da basu da tsafta.

6. Ana iya kamuwa da cutar wajen amfani da abin hujin kune ko kuma abinda ake zanen jiki da shi wanda ake kira da turanci ‘tatoo equipment’.

Hukumar ta ce baza a iya kamuwa da cutar ta hanyar amfani da cokali,kofi, rike hanu, sunbar wanda ke dauke da cutar ba.

Bayan haka hukumar ta bayana wasu alamomin gane cutar kamar haka;

1. Yawan ciwon kai.

2. Yawan jin gajiya a jiki.

3. Rashin cin abinci.

4. Yawan samun ciwon gabobi

5. Ciwon ciki.

6. Yawan yin amai.

Hanyoyin da za a bi domin guje wa cutar Hepatitis.

1. Amfani da tsafatacen ruwa sannan a tabbatar ana wanke ganyayyakin da ake ci da kayan lambu da ruwan gishiri kafin a ci.

2. Yin allurar rigakafin cutar musamman ga matafiya.

3. A dunga amfani da kororo roba idan za a yi jima’I sanna a rage yawan wadanda ake yi da su.

4. Tsaftace muhalli musamman ban daki.

5. Samun cikakken bayani akan cutar sannan kuma da wayar da kan mutanen da basu da masaniya akan cutar.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Yan Nijeriya sun sayi katin waya sama dana tililiyan uku a 2017

Wani bincike ya nuna cewa duk da halin kunci na tattalin arziki, ‘yan Nijeriya sun yi amfani da kudaden cefanen gidajensu wajen sayen katin buga waya har na sama da Naira Tiriliyan uku a shekarar da ta gabata.

Yan bindiga sun kashe Mutane 25 a Kauyukan jihar Zamfara

Wasu yan bindiga da ake kyautata zaton barayi ne sun kashe a kalla mutane 25 a wani hari kan kauyuka biyu dake karamar hukumar Birnin Magaji ta jihar Zamfara.

Mazauna yankin sun bayyana cewa wasu yan bindiga dake kan babura sun bude wuta kan wasu manoma dake girbin dankali a kauyen Garin Halilu inda suka kashe mutane tara nan take.

Bayan haka da misalin karfe biyar na yamma lokacin da ake hada gawarwakin mamatan sun dawo kauyen inda suka kashe karin wasu mutane uku.

“Daga nan suka cigaba ya zuwa kauyen Gidan Kaka mai makotaka da kauyen inda suka kashe mutane tara a can, ragowar mutanen hudun da aka kashe sun fito ne daga kauyen Nasarawa Godel wadanda suka kai dauki ga mutanen kauyen Gidan Halilu dake fuskantar hari,” wani mazaunin kauyen Tukur Godel ya shedawa jaridar Daily Trust.

Amma kuma mai magana da yawun rundunar ƴansandan jihar, SP Muhammad Shehu ya bayyana cewa mutane biyar aka kashe a harin kuma tuni al’amura suka cigaba da gudana bayan harin da yan bindigar suka kai.

Dalibar Jami'ar Usman Danfodiyo ta samu makin da ba'a taba samu a shashen ilimin physics

Kamar yadda ake cewa “duk abin da namiji zai iya, mace za ta iya yin fiye da hakan”, wata daliba mai suna Zainab Bashir ta kammala karatunta da maki (CGPA 4.93), wanda shi ne maki mafi girman da ba a taba samu ba a gaba dayan tarihin sashen ilimin Physics na Jami’ar Usman Danfodiyo, Sakkwato.

Wani Matashi yayi ma Ecobank kutse inda ya saci Naira Miliyan 207

An gurfanar da wani matashi dan shekaru 28 a gaban kuliya a sakamakon tuhumar shi da ake yi da yin kutse a manhajar bankin Eco inda ya saci Naira miliyan 207.

Matshin mai suna James Nwagalezi ya aikata wannan laifi ne tare da wani mai suna Okoli Nmesoma, wanda tuni aka fara yi masa shari’a.

Dan sanda mai kara, Insfekta Jimoh Joseph ya fadawa kotun cewa matashin tare da wasu da yanzu haka ake neman su sun aikata laifin ne a ranar 27 ga watan Afrilu a yankin Okokomaiko da ke Ojo a jahar Lagos.

Ya ce bankin ne ya kai karar faruwar lamarin ga DPO na ofishin ‘yan sandan Ikoyi, Tijjani Mustapha, inda daga nan ne aka shiga neman su.

Bayan da aka shafe watanni ana nema ne aka kama Nwagalezi, wanda shi ne na 6 a jerin wadanda aka kama game da laifin.

Lafiin ya saba da sashe na 411, 387, 287 da 325 na kundin dokar jahar Lagos.

Sai dai Nwagalezi bai amsa laifin ba.

An bada belin shi akan Naira miliyan daya, tare da bukatar masu tsaya masa guda biyu.

An daga sauraren karar zuwa ranar 4 ga watan Yuli.

Rikicin Ma'aurata tsakanin hausawa

Abu ne sananne cewa a wannan zamani, duniyar Bahaushe – har da ta wanda ba Bahaushe ba – ta cika da rikita-rikita da rikice-rikice tsakanin ma’aurata. Aure kuwa abu ne mai muhimmanci wanda ya kamata a gina shi kan soyayya da kauna. To amma wace irin soyayya? Ba soyayya ta shakaka ba; soyayya ta hakika. A yanzu, lamarin yana da takaici matuka!

Za ka ga kafin a yi aure, ana ta soyayya tiryan-tiryan kamar ba gobe. Amma da zarar an yi aure, sai husuma ta fara tashi kamar wutar daji. To ita wannan matsala idan mutum zai dauki matakai na kiyaye ta, to zai iya kawar da su daga gare shi cikin ikon Allah. Wannan makala za ta amfani kowa – Musulmi ko Kirista.

Da farko, auren mace don kyawun fuskarta yana da matukar illa, domin bayan an yi aure, kyawun zai iya gushewa. Shi ke nan kuma! Da ma don kyawun aka yi auren, yanzu kuma babu kyawun. To a nan sai soyayya ta dawo tsana. Koman kyawun ‘ya mace, mafi akasari tasirinsa kafin ta yi aure ne – tana yin aure, kyawun halinta ne zai yi tasiri. Saboda haka kar kyau ya zama ma’auninka na auren mace. Na yi amanna cewa wannan shawara ba Musulmi kadai za ta amfana ba, har da Kiristoci.

Bugu da kari, shi rikici ba a rasa shi kwata-kwata a tsakanin ma’aurata. To idan aka samu wannan dan rikici, ba shi ke nuna cewa aure ya zo karshe ba. Akwai hanyoyin shawo kan matsalar. Muhsin Ibrahim, malamin harshen Hausa a Jami’ar Cologne da ke Jamus, ya bankado yadda lamarin yake, inda ya ce: “Sirrin zama da iyali cikin farin ciki ba abu ne boyayye ba. Rikici kuwa abu ne da ba a rabuwa da shi, wanda ke sauya rayuwar kunci ta koma ta farin ciki.” Ya kara da cewa: “Kar dai a bar rikicin ya yi kamari. Ku hadu domin tattauna matsalolinku.” Ka ga ke nan a kullum tattaunawa na da muhimmanci domin ta hanyar haka ne kowa zai gano matsalolin kowa.

Kuma wasu lokutan, tun kafin a yi auren, auren yake wargajewa. Ba komai ke janyo haka ba sai aikata abubuwan da ba su halatta ba a tsakninku kafin aure. Shi ya sa za ka ga bayan an yi aure, kowa na zargin kowa; kowa yana yi wa kowa kallon hadarin kaji. Ita matar babu hali mijinta ya fita waje sai ta zarge shi da aikata irin abin da suka saba aikatawa kafin su yi aure. Haka shi ma mijin. Daga karshe, sai ka nemi auren ka rasa.

Idan ba a dauki mataki ba, adadin zaurawa tsakanin al’ummar Hausawa sai ya fara gogayya da adadin ‘yan mata, wadanda ba su taba yin aure ba, domin saki ya zama ruwan dare a yanzu. Kuma wani abin bakin ciki shi ne: za ka samu abin da ke kawo sanadin sakin bai taka kara ya karya ba. ‘Yar matsala kadan saki, saki, saki! To idan ka sake ta fa, a banza za ka dinga kashe kudin da kake samu na albashinka.

A karshe, babban maganin duk wata matsala shi ne “HAKURI”.

Muhammadu Sabiu ne ya rubuto wannan makala daga Bauchi. 09078713542

Sunday, 23 December 2018

TARIHIN HAUSAWA


TARIHIN KABILAR HAUSA

Kabilar Hausa dai,kabilace dake zaune a arewa maso yammacin taraiyyar Najerya da kudu maso yammacin jamhuriyyar Nijar , Kabilace mai dimbin al'umma, amma kuma a al'adance mai mutukar hadaka, akalla akwai sama da mutane miliyan hamsin da harshen yake asali gare su. A tarihance kabilar Hausawa na tattare a salasalar birane.Hausawa dai sun sami kafa daularsu ne tun daga shekarun 1300's, sa'adda suka sami nasarori da dauloli kamar su Daular Mali
Songhai,Borno da kuma Fulani . A wasu lokutan
Hausawa sun sami gagarimin ikon, mulki da hadaka ta kau da baki'yan neman ruwa da tsaki,da kuma neman angizon a cikinta da kuma harkallar bayi. A farko- farkon shekaru na 1900's, a sa'adda kabilar Hausa ke yinkurin kawar da mulkin angizo na fulani,sai turawan mulkin mallaka na Birtaniya suka mamaye
arewancin Nijeriya , da kuma kafa manufofin mulkin bayan gida,a bisa karkashen mulkin birtaniya,'yan mulkin mallaka sai suka marawa fulani baya na cigaba da manufofin angizon siyasarsu, har yanzu dai mulkin kamin gambiza tsakanin Hausawa da Fulani shi ne yayi kane-kane a arewacin Nijeriya. Wannan hadakar gamin kambiza, an farota ne tun asali a matsayin fulani su dare madafun ikon a tsararren tsarin siyasar arewa.Akasarin masu mulki na fulani sun kasance yanzu, a al'adance hausawa gwamitse Ko da yake, Hausawa na farko-farko maharba ne, amma ya zuwan addinin islama da kuma karbansa da hannu bibbiyu ya sanya labari ya sha bambam.Ginshikokin al'adun hausawa na da mutukar zaranta, kwarewa da sanaiya fiye da sauran al'ummar dake kewayenta. Sha'anin noma ita ce babbar sana'ar hausawa inda hausawa ke ma sana'ar noma kirari da cewa, na doke tsohon ciniki kowa yazo duniya kai yatarar, akwai kuma wasu sana'o'in kamar su sha'anin jima watau harkar fatu, rini, saka da kira, fannonin dake mutukar samun cigaba a harkokin sana'o'in hausawa. Hausawa dai sun jima da shahara wajen harkar fatauci kana kuma masu arziki na taka rawa a sha'anin yau da kullum, tare da masu mulki da masana. Harshen
Hausa shi ne mafi girma da kuma mafi sanai'yar harshe a nahiyar Afirka, harshen hausa ya aro wasu kalmomi daga wasu harsuna musamman larabci kana kuma harshen na tafiya tare da yanayin mu na zamani bisa al'adar cudeni- na cudeka. Harshen Hausa dai ya zama harshen yau da kullum ga miliyoyin jama'a da ba hausawa bane a nahiyar Afirka . Bugu da kari, akwai cincirindon al'ummar Hausawa a manyan biranen yammacin Afirka da arewacinta da kuma yankunan cinikayyar al'ummar Hausawa da kuma yankunan da Hausawa suka jima suna bi a hanyar ta zuwa aikin hajji. Akwai kuma rubutattun adabi masu zurfi da kasidodi da kuma rubuce-rubuce a rubutun ajami da aka buga tun kafin zuwan turawa yan' mulkin mallaka na birtaniyya. Har ila yau, kuma wani tsarin rubutu a ajame da aka kirkiro tun kafin zuwan turawa, da ba kasafai ake amfani da shi ba yanzu.

Yadda zaka samu Maki 280 a jamb

Assalamu Alaikum, wadannan shawarwarine da babu shakka idan dalibi ya bisu sau da kafa to Insha Allahu zai samu gagarumin maki a jaraba...