Adthis

Yadda Zaka Goge Bashin Dakaci A Kowani Layin MTN Batareda Kosisin Ka Ba

Monday, 28 January 2019

Aure Bautar Ubangiji

AURE BAUTAR UBANGIJI
=
Wannan shine bayani na shida:

_Bayan haka in ba'a mantaba har yanzu dai muna cigaba da bayanin irin mazajene wadanda sukafi alheri wadanda sukafi cancanta abasu aure****_
      _Abaya munji labarin Auren julaibib dakuma albarkarda matar tasamu da ribarda taci na aurenshi duk da cewa bashida ko sisi be ajje ba beba kowa ajiya ba kuma gashi mummuna amma kunji dai irin alherinda yabiyo baya wanda hatta iyayen nata su kansu sunyi alfahari da wannan aure sunji dadinshi har suka koma ga Allah suna farin cikin wannan aure,****_
        _To amma yanzu a wannan zamanin semuka juyarda abin muka zama babu ruwanmu da bin waccan wasiyyar ta manzon Allah, takaimu ga yau iyaye har bin bokaye sukeyi akan sunaso wai ajuyo musu hankalin wani dan yazo yanemi 'yarsu dan su samu damarda zasu tatsi dukiya ajikin wancan mutumin***_
         _Yau takaimu ga har abun yazama gasa akeyi wajen cewa anaso 'yata dole seta auri mijinda zata kece raini wanda ze siya mata mota yasiyawa iyayenta gida koda kuwa wannan dukiyar tashi bata halas bace****_
         _Iyaye a yau babu ruwansu kawai duniya suke dubawa yaki halas yaki haram sudai kawai burinsu shine wai sukai 'yarsu inda zasu huta, can kenan abakinsu suke fadar haka****_
    _To wannan irin qazamin ra'ayin namu damuka riqe a yau na cewa bazamu bayarda aure ba se ga wanda yake da dukiya dan kawai musamu duniya, amma idan mutumin kirki me addini yafito neman auren 'yarmu to lallai Annabi (s.a.w) yace mubashi aure, inkuwa muka hana to 6arna zata yadu abayan qasa da fitina, wanda kuma gatanan yanzu haka muna gani, fitinar yau daban ta gobe daban, wanima idan ka aura masa 'yar taka seya maida ita tamkar baiwa kodai yayita jibgarta kokuma yariqa zaginka agabanta kokuka yadinga daura mata hidimarda yasan cewa tafi qarfinta, hakanan ze dage yayita bautarda ita, kuma babu ruwanshi da biyan buqatunta ta kowanne bangare*****_
       _Wani zaka ganshi a waje akwai walwala ga kyauta iri iri dan neman suna, yau kajishi ance ya kashe wasu maqudan kudi can, gobe kajishi yakai kudi can, yau kaji yasaima wane mota gobe ace ya siyama wane gida, hakanan zakaji yanata faman rarraba kyaututtuka, amma itako wannan matar tashi idan kaji irin halinda take ciki na qunci da yunwa zakayi mamaki, amma wannan matsalar ba lokacinta bane yanzu dan haka zamu jingineta se can gaba idan mukazo shafinta****_
=
_Wannan fitintunu da Annabi (s.a.w) yake cewa zasu watsu abayan qasa idan ana hana irin wadannan mazaje aure, to daga cikin fitintunun fa akwai wadda ake samun kangara tsakanin iyaye da 'ya'yansu kaga ansamu takun saqa, saboda ita dai 'yar mafi yawa tasani cewa bawai son Allah da manzonshi bane yasa iyayenta suka qi amincewa ta auri wannan bawan Allah wanda ita tana kyautatamasa zaton cewa mutumin kirkine, kawai wani kwadayin duniya shine yasa sukaqi yarje masa subashi aurenta kokuma wani ra'ayi nasu na can daban, amma mafi yawa idan kaga ansamu irin wannan matsalar to zakaga iyayen mafi yawa ba saboda Allah da manzonshi suke qoqarin hanata wanda takeso ba saboda wata manuface tasu****_
      _To daga wannan lokacinda wadannan iyayen sukayi hakan to shikenanfa sun qunsa bakin ciki a zuciyar wannan 'ya tasu, sekaga wata dalilin haka ta fada ga zinace zinace, wata sekaga ta kangarema iyayen bata musu biyayya kokuma ta auka ma shan miyagun qwayoyi kokuma ta auka cikin wannan bala'in na madigo wanda yazama fitina ga musulmai ahalin yanzu****_
          _To lallai 'yan uwa daga cikin hanyoyinda zamubi mu yaqi matsalar zinace zinace da madigo acikin wannan al'umar tamu, shine aduk sadda mutumin kirki bawan Allah me addini da kyawawan dabi'u yafito neman auren 'yarmu to lallai mubashi kada tunanin wani abin duniya wanda ba me dorewa ba, yasa muhanashi bayan kuma shi yanason yarinyar itama tana sonshi****_
=
=
Zamu dakata anan sekuma bayani nagaba idan Allah yakaimu
=
_Almajirinku ne kamar kullun, dan mutanen Kabo_
.
```Jameel Alhassan Haruna kabo```
.
_(Alwahhaby, Assalafy)_
.
.
Allah ta,ala yasa mudace.mahuta.com.ng

Tuesday, 15 January 2019

Yadda Zaka Nemi Aikin Zabe(Ad-hoc Staff)

Yadda Zaka Nemi Aikin Zabe Na 2019.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta saki form na neman aikin zaben shekara 2019.

Neman aikin yakasu zuwa biyu:
• Ma’aikatan wucin Gadi (Adhoc Staff – RATECH)
• Ma’aikatan INEC na dindin din (LGATECH)

Ana iya rijistar wannan ayyuka guda biyu a shafin INEC na yanar gizo wato pres.inecnigeria.org Sai dai kuma ba kowa zai ci gajiyar aikin ba, har sai mutun ya cika ka’idojin da sashen fasaha na hukumar zaben ya gindaya.

Sharudan Rijista Dan Zama Adhoc Staff – RATECH
Mutane Kala uku ne za su iya rijistar wannan aikin.
1. Wanda ya yi bautar kasa da hukumar INEC tsakanin 2013 zuwa 2018 (Ex-coper)
2. Ma’aikacin hukumar INEC mai Karamar diploma zuwa sama. Ya zamana yana da ilimin na’ura mai kwaqwalwa.
3. Dalibin jami’ar tarayya ko kwaleji ko poly wanda saura shekara daya ya gama karatu. Shi ma sai yana da ilimin na’ura mai kwakwalwa.

Abubuwan Da zaka tanada
• Dole ne ya zama kana da lambar waya da kuma email address
• Referral letter daga ma’aikacin gwamnati da ya taka matsayin aiki na GL14 zuwa sama.
• Hoton ID card.

Sharudan Rijista Dan Zama INEC Staff – LGATECH
• Iya ma’aikacin INEC mai ordinary national diploma zuwa sama zai iya register. Shi ma sai yana da ilimin na’ura mai kwakwalwa.
• Dole ne ya zama kana da lambar waya da kuma email address
• Hoton ID card.

Sunday, 13 January 2019

An Kama Masu Daukar Nauyin Yan Ta'adda a Jihar Zamfara

 1. ANKAMA MAYAN 'YAN KASUWAR DAKE DAUKAR NAUYIN 'YAN BINDIGAR ZAMFARA A JAHAR

  - 'Yan sanda sun kama wasu mahauta 'yan asalin jihar Zamfara mazauna Legas bisa zarginsu da daukan nauyin 'yan bindigar Zamfara
  - Mahautan guda hudu da aka kama sune Alhaji Ago Atine, Alawani Abubakar, Mohammad Sahagari da Bashir Aliyu
  - Alhaji Altine ya ce wani Alhaji Naira ne ke sayar masa da shanun da araha shi kuma ya sayar da su da tsada a Legas
  - Sashin tattara bayanan sirri na 'yan sanda ya gano cewar 'yan bindigan na amfani da kudin da suke samu daga sayar da shanun satar ne wurin sayo makamai

  Rundunar 'yan sandan Najeriya ta kama wasu mahauta hudu da ke sayar da nama a Agege na jihar Legas bisa zarginsa da daukan nauyin 'yan bindiga da ke kai hare-hare a wasu garuruwa a jihar Zamfara.

  The Punch ta ruwaito cewa garuruwan da aka kai harin sun hada da kananan hukumomin Tsafe, Zurmi, Shinkafi Maradun, Mari da Birnin Magaji.
  'Yan sandan sunyi ikirarin wadanda ake zargin su ke samarwa 'yan bindigan kudaden da sukae sayan makamai ta hanyar sayan shanun sata daga hannunsu. Wadanda ake zargin sune Alhaji Ago Atine, Alawani Abubakar, Mohammad Sahagari da Bashir Aliyu.

  An gano cewar 'yan bindigan da suka kashe mutane da dama sunyi amfani da kudin da suka samu bayan sayar da shanun ne wajen sayo bindigu da wasu muggan makamai daga kasar Libya.
  Majiyar Legit.ng ta gano cewa sashin tattara bayyanan sirri na 'yan sandan Najeriya sun damke kwamandan 'yan bindigan ne a Zurmi kuma ya tona yadda 'yan bindigan ke samun kudin sayan makamai.

  An kama wadanda ake zargin su hudu ne yayin da suke kokarin sayar da wasu daga cikin shanun satar ga wani mutum.
  Daya daga cikin wanda ake zargin, Alhaji Altine ya shaidawa City Round cewa ya saya shanu fiye da 400 daga wani Alhaji Naira. Sai dai ya ce bai san cewa shanun sata bane.

  Ya ce, "Alhaji Naira ya aiko min da shanu fiye da 400 ni kuma na sayar masa a mayanka. Na tura kudin zuwa asusun ajiyar bankin Alhaji Naira. Na saya shanun da araha, ya sayar min da kowanne guda a kan N60,000 zuwa N70,000 ni kuma na sayar da kowanne a kan N170,000 zuwa N180,000. Ban san abinda Alhaji ya ke yi da kudin ba kuma ban san shanun 

Thursday, 10 January 2019

Yadda Za Kai Rijistar Jamb Cikin Sauki


kamar yanda koya ya sani yau ne ranar da hukumar jarabawar shiga jami'a wato Jamb suka fitar a matsayin ranar fara registration na wannan shekarar.. 


After successful payment & obtaining the JAMB ePIN, the candidate would proceed to any of the accredited CBT Centres to complete his/her own registration . Remember, at this point, the ePIN would have been delivered electronically to candidates and not to be handwritten. It would be delivered directly to the phone number used to create your profile code.

At the CBT Centre, The candidate presents the ePIN at any JAMB accredited CBT Centre for validation and completion of registration for 2019 UTME. Candidate is expected to pay NOT more than N700.00 as Service Charge to the CBT Centre.

Once payment has been made to the CBT Centre, candidate Provides:

(i) Biodata: Date of Birth, Nationality, LG/State of origin, Gender, e-mail address, telephone

(ii) Choice of institutions & programmes (Disciplines)

(iii) Qualification with grades/dates, if not Awaiting Result

(iv) UTME subjects & Choice of Examination town for

(a) Mock examination (optional)

(b) Examination for UTME (actual examination)

A proper template that you can fill with parents & guardians, before heading to the CBT Centre, will be provided to you tomorrow, so ensure you check back on Myschool website to download it for free.

Before proceeding to the CBT Centre to register, candidates are advised to use the 2019 JAMB Brochure , to confirm the courses they intend to study, requirements and schools that offer such courses, to avoid time wasting.

Above all, get the 2019 JAMB CBT Practice Software or the 2019 Myschool JAMB CBT Practice App . These will enable you to cover all JAMB past questions as well as get familiar with the JAMB CBT environment before the exam.

Please note that while at the CBT Centre, you would be required to;

Do picture capture (no scanning of passport photography)

Do Biometric enrollment (10 fingers)

Review entries & confirm correctness

Print Registration Slip only by USING BIOMETRIC AUTHENTICATION to confirm valid finger-print (UTME+DE)

Collect reading text & CD

THERE WILL BE NO OFFLINE REGISTRATION, as all accredited CBT Centres have been empowered for real time online registration

Please note that you would be able to Upload of O’ level and A’ level results at the CBT Centre. This will be done by the candidate at the JAMB Portal.

Schools, Institutions, Tutorial Centres, Business Centres & Cafes can equally act as JAMB CBT Agents and Training Centres to help train students for the upcoming exams.

Tuesday, 8 January 2019

Abinda INEC Za Ta Biya Maaikatan Zabe (Ad-hoc Staff)

Kamar yadda ta saba a lokacin zaɓe. Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC), a wannan Karon ma, za tayi anfani da yan bautar kasa (Copers), da kuma ɗaliban Jami'o-in Gwamnatin Tarayya, a matsayin jami'an zaɓe, domin gudanar da zaɓen shekara ta 2019. 

Hukumar ta bayyana cewa, kaso Arba'in na wanda za su gudanar da zaɓen yan bautar kasa ne (Copers). Inda ta ke da mazaɓa 119,809 kuma akwai yiwuwar za ta kir kiri mazaɓa 30,000. 

Ga abin da za ta ba kowana jam'i. 


An Cimma Yarjejeniniya Tsakanin ASUU Da Gwamnatin Tarayya

Bayan Kammala Zama Da ASUU Sukayi Da Gwamnatin Tarayyar Nigeriya Shugaban Kungiyar Yace Zasu Sanar Da Matsayar Su A Kowanne Lokaci Kodai Sujanye Daga Yajin Aikin Ko kuma Su Cigaba.

Gwamnatin tarayya ta yi alkawarin zata biya kungiyar ASUU kudade kimanin naira biliyan goma sha biya (15 billion) domin cika musu alkawarurrukan da aka daukar musu a shekarun baya wanda dama rashin cika alkawarin ne maƙasudin yajin aikin.

Kungiyar ASUU ta Wallafa a shafinta na tuwita cewa zasu janye jayin aikin ne kawai bayan sun zauna da sauran mambobinsu na kungiya inda daga nan ne zasu yanke cewa su ci gaba da yajin aiki ne ko kuma zasu janye.

Monday, 7 January 2019

Yadda Zaka Samu 4GB Kyauta A layin Airtel

Kamfanin Airtel na bada Kyautar Data har 4GB sai dai a yanzu haka mutanenmu basu farga da wannan tsarin ba domin a wasu yankunan har wasu sun fara siyar da tsarin ga mutane.

Hausawa sunce raba arne da makami jihadi ne don haka dole mu yiwa jama’a bayani.

Rubutuka Masu Alaka:

[Kayi Register Yanzu] Yadda Ake Samun Kudi Ta YouTube

[Kayi Register Yanzu] Taron Horaswa Akan Yadda Ake Yin Talla A Facebook

Yadda Ake Samun Wannan Data Shine:
Zaka sayi layin MTN mai 3G sai kayi Register.

Daga nan sai ka saka a waya mai 4G.

Shikenan zakaji alert na kyautar MB din ya shigo wayarka kamar yadda kuke gani a hoton dake kasa:

Bahaushe Ya Kirkiri Bokitin Dafa Ruwan Zafi

Lallai kam fasahar Arewa sai Dan Arewa, a daidai lokacin da mafiya yawancin alummar Nigeria suka maida bokitin Fenti a mazaunin kwandon bola ko shara da kuma tara ruwa.

Abin yasha ban-bam ga wani matashi dan asalin jihar Kaduna, inda yake amfani da robobin Fentin wajen dafa bokitin ruwan zafi.

Wato abinda ake Kira “Electric Bucket Heater” a hausar sarauniyar ingila.

Hotunan Irin Wannan Bokitan:

Saturday, 5 January 2019

Cikakken Tarihin Malama Aisha Lemu (Allah yayi mata Rahama)

A yau, Asabar, 5 ga watan Junairu, 2019, Allah ya yi wa babbar malamar addinin Musuluncin nan ‘yar asalin kasar Birtaniya, Bridget Aisha Lemu, rasuwa. Malamar ta rasu tana da shekaru 78 a duniya.

Malama Bridget A’isha Lemu, wadda ta kasance fitacciyar marubuciyar littafan addinin Musulunci, baturiyar kasar Birtaniya ce wadda ta karbi addinin Musulunci a shekarar 1961.

An haife ta a garin Poole na kasar Ingila a shekarar 1940. A’isha ta soma wasuwasi a kan addininta na farko tun tana shekaru 13. Hakan ne ya sa ta soma bincike a kan wasu addinai kamar addinin Hindu da kuma Buddha na kasar Chana. Ta yi karatu a jami’ar birnin Landan karkashin makarantar nazarin mutanen gabashin Asia da Afirka, ‘School of Oriental and African Studies (SOAS)’, inda ta maida hankali a bangaren tarihi, yare da kuma al’adun kasar Chana. A lokacin da take can ne ta hadu da wasu Musulmai da suka damka mata adabin addinin Musulunci domin ta karanta. Hakan ya sa ta karbi addinin Musulunci a cibiyar addinin Musulunci a shekarar 1961.

Musuluntarta ke da wuya ta taimaka gurin kafa kungiyar mabiya addinin Musulunci a jami’ar, inda ta zamo sakatariyar kungiyar ta farko. Bayan nan kuma ta taimaka gurin kafa tarayyar kungiyoyin dalibai mabiya addinin Musulunci.

Bayan kammala karatu a SOAS, Aisha Lemu ta koma digiri na biyu a bangaren koyar da yaren Turanci a matsayin yaren kasar waje. A lokacin da take karatun ne Allah ya hada ta da mijinta, Sheik Ahmad Lemu, wanda shima yake karatu a wata kwalejin jami’ar Landan, sannan kuma shima yake ayyukan yada addinin Musulunci a kwalejin.

Bayan ta samu kwalin digirinta na biyu a fannin koyarwa sai ta taho jihar Kano ta kasar Nijeriya a watan Agusta 1966 domin ta yi aikin koyarwa a makarantar koyon yaren Larabci, inda Sheik Ahmad Lemu yake a matsayin shugaban makarantar. Sun yi aure a watan Afrilu, 1968, inda A’isha ta zamo matarsa ta biyu. Bayan nan A’isha ta koma Sakkwato inda ta zamo shugabar makarantar ‘yan mata ta gwamnati.

A shekarar 1976 Sheik Ahmad Lemu ya zamo shugaban alkalan kotun daukaka kara ta addinin Musulunci a jihar Neja, yayin da Aisha take shugabar kwalejin mata da ke Minna. Ma’auratan sun kafa gidauniyar ilimin addinin Musulunci “Islamic Education Trust (IET)” wadda take da rassa a jihohin Nijeriya da dama. IET na da ofisoshi da dakunan karatu da cibiyoyin karatun manyan mata. A’isha ta kasance mamba na kwamitin ilimin addinin Musulunci, wanda hukumar bincike da bunkasa ilimi ta Nijeriya ta kafa domin yin bitar manhajar darasin ilimin addinin Musulunci na makaratu.

A shekarar 1985, A’isha ta samar da tarayyar kungiyoyin mata Musulmai (FOMWAN) inda aka zabe ta a matsayin Amirar kungiyar ta farko. Ta shafe shekaru hudu cur tana shugabantar kungiyar.

Wasu daga cikin ayyukan da ta wallafa sun hada da:

– A student’s introduction to Islam. Macmillan Education, London 1971.
– Gabatar da addinin Musulunci ga dalibi.
– Northern Nigerian Pub. Co., Zaria 1976.
– Islamic citizenship and moral responsibility. Islamic Education Trust, Minna 1979.
– Students’ Islamic Society Branch Organization (Islamic Education Trust Guidelines series). Islamic Education Trust, Minna 1979.
– Methodology of primary Islamic studies. A handbook for teachers. Islamic Publications Bureau, Lagos 1980.

– A critical look at the theory of evolution (=IIFSO 46). International Islamic Federation of Student Organizations, Salimiah [Kuwait] 1982.
– A degree above them. Observations on the condition of the northern Nigerian Muslim woman. Islamic Education Trust, Minna and Gaskia Corporation respectively, Zaria 1983.
– The theory of evolution from the Islamic perspective (=International Islamic Federation of Student Organizations, p. 46). Translated by Ayisha Niazi. IIFSO, Salimiah (Kuwait) 1983.
– Tawhid and fiqh. Belief and jurisprudence (= Junior Islamic studies. Book 1). Islamic Education Trust, Minna.
– Lessons on the Qur’an (=Junior Islamic studies, Book 2A). Hudahuda, Zaria and Hodder & Stoughton, London 1986. ISBN 0-340-32791-X.
– Junior Qur’anic Arabic (=Junior Islamic studies . Book 2B). Hudahuda in association with Hodder and Stoughton, Sevenoaks, and Zaria, 1986. ISBN 0-340-32790-1.
– Tahdhib (moral education) and Sirah (=Junior Islamic studies . Book 3). Islamic Education Trust, Minna.
– The Ideal Muslim Husband . Islamic Education Trust (Publications Division) Minna 1987. Reissue at Al-Saadawi Publications, 1992. ISBN 1-881963-03-9
resp. ISBN 978-1-881963-03-5 .
– Islam, the religion of the future. The Islamic Union of Hong Kong, Hong Kong 1988.
– Islamization of Education. A Primary LevelExperiment in Nigeria. In: Muslim Education Quarterly, volume 5 No. 2, 1988.
– The role of Muslim women in the 15th century Hijrah. In: Ramatu Abdullahi, Muslim Sisters Organization of Nigeria (eds.): The Muslim woman. Challenges of the 15th Hijra . Woye & Sons, Ilorin and Islamic Publications, Lagos 1988. *** ”
– Gari ya waye (Nazari a kan matsayin mata Musulmi a Arewacin Najeriya). Translated by Shuayb Haruna Gambo Langen. Mosque Foundation, Kaduna 1989.
– Islamic studies for senior secondary schools. Book 1. Islamic Publications Bureau, Lagos 1989. ISBN 978-2470-27-9 .
– Islamic studies for senior secondary schools . Book 2. IET, Minna 1990.
– Muslim women and marriage under the Shariah rights and problems faced. In Awa U Kalu and Yemi Osin Bajo (ed.): Women and children under Nigerian law (=Federal Ministry of Justice, Law Review series Vol. 6.). Federal Ministry of Justice, Lagos, 1990. ISBN 978-2439-06-1.

– Laxity, moderation, and extremism in Islam. Islamic Education Trust, Minna,
1991. ISBN 978-30722-2-6.
– The Ideal Muslim Wife. Islamic Education Trust (Publications Division), Minna 1992. ISBN 978-2159-06-9.
– Animals in Islam. Spectrum Books, Ibadan and Islamic Education Trust, Minna 1993. ISBN 978-2462-33-0.
– Laxisme, modération et extrémisme en Islam (= Occasional papers. 5). Translation of Michèle Messaoudi.

International Institute of Islamic Thought, Herndon, Virginia, and London, 1995. ISBN 0-912463-96-1.
– Islam and Alcohol. Edited version of a lecture delivered at Advanced Teachers’ College Minna on the occasion of Id-al-Maulud, February 1981. Al-Saadawi Publications, Alexandria (Virginia) 1996. ISBN 1-881963-02-0.

– Islamic ‘aqidah and fiqh. A textbook of Islamic beliefs and jurisprudence . IQRA’ International Educational Foundation, Chicago 1996. ISBN 1-56316-061-7. Sikap ekstrem. Penyakit dakwah Islam. International Institute of Islamic Thought, Petaling Jaya 1996.
– Islamic tahdhib and akhlaq. Theory and practice. IQRA’ International Educational Foundation, Chicago, 1997. ISBN 1-56316-320-9.

– A holistic approach to teaching Islam to children. A paper presented at the Conference on Private Islamic Schools, 12–13 August 1994, held in Minna by the Islamic Education Trust on behalf of the Nigerian Da’wah Coordination Council (NDCC). IET Publications Division, Islamic Education Trust, Minna, 2001. ISBN 978-2159-45-X.

– Child upbringing and moral teaching in Islam. A paper presented at Abuja Muslim Forum Seminar on Child Upbringing, a Divine Obligation, a Complementary Responsibility, December 1977 . Islamic Education Trust, Minna, 2001. ISBN 978-2159-44-1.

– Teaching for tolerance in Nigeria . In: Recep Kaymakcan, Oddbjørn Leirvik, Oslo Coalition on Freedom of Religion or Belief (eds.): Teaching for tolerance in Muslim majority societies . Center for Values Education (DEM) Press, Istanbul, 2007. ISBN 978-975-6324-98-1

Allah ya ji kan Malama Aisha Lemu

Friday, 4 January 2019

Ko Kasan Wa Ce ce Ladi Kwali??


Ladi Kwali, Fasihiya ce, kwararriya, ‘yar baiwa, mai kyakkyawan tunani a kirkira.
An haifi Ladi Kwali a kauyen Kwali da ke a kasar Gwari, wanda yanzu haka take a arewacin Nigeria, A shekarar 1925.
Tun tasowarta, Ladi ba malalaciya ba ce, ba ta yarda da zaman kashe zani ba. Wannan ya sa, tun tana kankanuwa, ta shiga harkar koyon yadda aka kera tukwane, da yake galibin yanki da ta taso, sana’arsu kenan.
Sannu a hankali, Ladi Kwali sai ta fara kwarewa wajen iya sarrafa tukwane, wadanda ake yin su da yunbu. Saboda mayar da hankali irin na Ladi Kwali, sai ya kasance, nan da nan, ta soma yin suna da fice a tsakankanin takwarorinta masu kera tukwane.
Sarkin Abuja na wancan lokacin, mutum ne mai son ire-iren wadannan tukwane, musamman ma wadanda aka kera su da kyakkyawan tsari, suka kuma yi kyau. Wannnan ya ba tukwanen Ladi Kwali da dama suka sami shiga cikin gidan Sarki. Allah cikin ikonsa, a irin wadannan tukwane ne, wani bature, ma’abocin kirkira, kuma mai kamfanin kera tukwane na Cardew’s Pottery Training Center, ya ga tukuwanen Ladi, ya kuma jinjina mata kwarai da gaske. Wannan kuwa ya faru ne a shekarar 1950. Lokacin Ladi tana da shekaru 25 kacal! A raye.
Yabawar da Bature Michael Cardew ya yi ga ayyukan kera tukwanen Ladi, ya ba ta damar shiga makarantar koyon yadda za a kera tukwane, wadanda ba ma na yunbu ba; wadanda ake kera su da abin da za a kira karfe da dangoginsa; kamar irin su alminiyon da dai sauransu.
Ladi Kwali, ita ce mace ta farko, a harkar kere-kere da ta fara kera kwanuka da kumbuna (irin na ado, a dakin amarya) da wasu irin kyawawan tukwane da ake kwalliya da su a wurare daban-daban.
Wani babban abin ban sha’awa, a harkar kere-keren Ladi Kwali shi ne, yadda take iya yin kwalliyar jan hankali jikin abubuwan da ta kera din, walau tukwane, ko kumbuna ko kwanuka da sauransu. Zane-zanen da wasu lokata, sukan ba mutane mamaki, da tunanin ya aka yi, Ladi ta yi su. Cikin wadannan mutane kuwa; har da Turawa da Larabawa da ma wasu manyan-manyan kabilu na duniya.
Ta dalilin Bature Mikael Cardew da kamfaninsa, aikace-aikacen Ladi Kwali ya ratsa kasashen Turai, musamman Kasar Burtaniya da Amurka. Wato dai, Ladi Kwali da aka haifa a kauyen Kwali a arewacin Nigeria, ta zama sananniya a tsakankanin kasashen da ke ganin sun fi sauran kasashe ci gaba, ta kowace fuska.
A tsakanin shekarar 1950 zuwa 1960, ayyukan kere-kere na Ladi Kwali, suka zama kan gaba, wato dai fiye da sauran ayyuka irinsu, (ciki kuwa har da na Turawan) a wani katafaren wajen da ake baje kolin irin wadannan kayan a Birnin London, mai suna Berkeley Galleries.
Ladi Kwali ta sami lambobin yabo da dama, a gida da wajen kasar nan. Ita ce dai macen da ta zama, ta fi kowace mace iya kerawa da tsara nau’o’in tukwane a kasar Nigeria. Babba daga ciki, ita ce, lambar yabo ta MBE, wadda ke nufin: Member of the Most Excellent Order of the British Empire (MBE).
A yanzu haka, wajen kere-keren tukwane da aka sani da Abuja Pottery, an sauya masa suna zuwa Ladi Kwali Pottery. Sannan a cikin Abujar yanzu haka, akwai babban titin da aka sanyawa sunanta. Bugu da kari, a bayan kudin Nigeria N20, hotonta ne, lokacin da take tsakiyar aikinta na kera tukwane.
Ladi Kwali ta rasu a shekara ta 1983. A lokacin tana da shekaru 58. Allah Ya jikanta da rahamarSa. Amin.

Kasar Laberia Ta Mayar Da karatun Jamia Kyauta Ga Yan Kasar

Shugaban Kasar Laberiya, George Weah ya tabbatar da cewa daga yanzu Jami’ar Laberiya da ma sauran Jami’oin gwamnatin kasar sun zama kyauta ga dukkanin wani dalibi dan asalin kasar wanda yake karatu a matakin digiri na farko a Jami’oin kasar.

Ko Gwamnatin Nijeriya Za Ta Iya Yin Haka?

Ko Me Yasa Jamaa Suka Fi Damuwa Da Rashin Auran Yan Finafinan Hausa?

A duk lokacin da aka bayyana wani aikin alkairi da ‘yar fim mace ta yi, sai ka ga maimakon a jinjina mata sai a dinga sauke sako dake nuna bacin rai game da rashin yin aurensu.

Wannan fa aiki ne babba, amma mu duba bangare daya zuwa biyu kawai!

Dukkanin masu nuna bacin ransu game da rashin auren
‘yan fina finan, mutane ne kawai dake son su a fuska, a
mafi yawan lokuta idan har mutum ya zo maka da irin
wannan zance a Inbox, da zarar ka tambaye shi shin kai
za ka aure ta? Amsa daya zuwa biyu zai ba ka. Farko:
A’a, ko kuma ta fi Karfina.

Amma kuma a haka za ka ga
ya dage a shafukan sada zumunta cewa su je su yi aure,
anya mace na iya auren kanta?

Duk da cewa ba kariya zan bai wa kowannen su ba, lallai illa ce babba macce ta yi wani girma irin na ‘yan shekaru
20 zuwa 30 ba ta yi aure ba, musamman idan har ta sami
miji nagari.

Ya kamata ‘yan finafinai mata ku gane gaskiya ta
hanyar auren mutanen da ke zuwa muku da niyyar aure,
domin mafi akasarin masu kallon finafinaku da kuma
masu nuna muku soyayya a shafukan sada zumunta
mutane ne da ba za su iya aurenku ba. Kun ga irin tasu
soyayya da suke nuna muku ita ce soyayya marar
amfani.

Allah ya ganar damu gaskiya ya bamu ikon aiki da ita.

Yadda Daliban Jami'ar Danfodio Sokoto Za Su Nemi Aikin Zabe (INEC) 2019

Yadda Daliban Jami’ar Dan Fodio Sokoto Zasu Nemi Aikin Zabe (INEC) 2019

Jami’ar Usman Dan Fodio dake Sokoto tana sanar da daliban jami’ar cewa ga duk mai sha’awar aikin hukumar zabe INEC na zaben wannan shekarar ta 2019 da ya hallara ranar Litinin 7, January 2019 a Centre for Islamic Studies dake City Campus tare da ID Card dinsa na makaranta da Admission Letter.

Yadda zaka samu Maki 280 a jamb

Assalamu Alaikum, wadannan shawarwarine da babu shakka idan dalibi ya bisu sau da kafa to Insha Allahu zai samu gagarumin maki a jaraba...