Adthis

Yadda Zaka Goge Bashin Dakaci A Kowani Layin MTN Batareda Kosisin Ka Ba

Monday, 28 January 2019

Aure Bautar Ubangiji

AURE BAUTAR UBANGIJI
=
Wannan shine bayani na shida:

_Bayan haka in ba'a mantaba har yanzu dai muna cigaba da bayanin irin mazajene wadanda sukafi alheri wadanda sukafi cancanta abasu aure****_
      _Abaya munji labarin Auren julaibib dakuma albarkarda matar tasamu da ribarda taci na aurenshi duk da cewa bashida ko sisi be ajje ba beba kowa ajiya ba kuma gashi mummuna amma kunji dai irin alherinda yabiyo baya wanda hatta iyayen nata su kansu sunyi alfahari da wannan aure sunji dadinshi har suka koma ga Allah suna farin cikin wannan aure,****_
        _To amma yanzu a wannan zamanin semuka juyarda abin muka zama babu ruwanmu da bin waccan wasiyyar ta manzon Allah, takaimu ga yau iyaye har bin bokaye sukeyi akan sunaso wai ajuyo musu hankalin wani dan yazo yanemi 'yarsu dan su samu damarda zasu tatsi dukiya ajikin wancan mutumin***_
         _Yau takaimu ga har abun yazama gasa akeyi wajen cewa anaso 'yata dole seta auri mijinda zata kece raini wanda ze siya mata mota yasiyawa iyayenta gida koda kuwa wannan dukiyar tashi bata halas bace****_
         _Iyaye a yau babu ruwansu kawai duniya suke dubawa yaki halas yaki haram sudai kawai burinsu shine wai sukai 'yarsu inda zasu huta, can kenan abakinsu suke fadar haka****_
    _To wannan irin qazamin ra'ayin namu damuka riqe a yau na cewa bazamu bayarda aure ba se ga wanda yake da dukiya dan kawai musamu duniya, amma idan mutumin kirki me addini yafito neman auren 'yarmu to lallai Annabi (s.a.w) yace mubashi aure, inkuwa muka hana to 6arna zata yadu abayan qasa da fitina, wanda kuma gatanan yanzu haka muna gani, fitinar yau daban ta gobe daban, wanima idan ka aura masa 'yar taka seya maida ita tamkar baiwa kodai yayita jibgarta kokuma yariqa zaginka agabanta kokuka yadinga daura mata hidimarda yasan cewa tafi qarfinta, hakanan ze dage yayita bautarda ita, kuma babu ruwanshi da biyan buqatunta ta kowanne bangare*****_
       _Wani zaka ganshi a waje akwai walwala ga kyauta iri iri dan neman suna, yau kajishi ance ya kashe wasu maqudan kudi can, gobe kajishi yakai kudi can, yau kaji yasaima wane mota gobe ace ya siyama wane gida, hakanan zakaji yanata faman rarraba kyaututtuka, amma itako wannan matar tashi idan kaji irin halinda take ciki na qunci da yunwa zakayi mamaki, amma wannan matsalar ba lokacinta bane yanzu dan haka zamu jingineta se can gaba idan mukazo shafinta****_
=
_Wannan fitintunu da Annabi (s.a.w) yake cewa zasu watsu abayan qasa idan ana hana irin wadannan mazaje aure, to daga cikin fitintunun fa akwai wadda ake samun kangara tsakanin iyaye da 'ya'yansu kaga ansamu takun saqa, saboda ita dai 'yar mafi yawa tasani cewa bawai son Allah da manzonshi bane yasa iyayenta suka qi amincewa ta auri wannan bawan Allah wanda ita tana kyautatamasa zaton cewa mutumin kirkine, kawai wani kwadayin duniya shine yasa sukaqi yarje masa subashi aurenta kokuma wani ra'ayi nasu na can daban, amma mafi yawa idan kaga ansamu irin wannan matsalar to zakaga iyayen mafi yawa ba saboda Allah da manzonshi suke qoqarin hanata wanda takeso ba saboda wata manuface tasu****_
      _To daga wannan lokacinda wadannan iyayen sukayi hakan to shikenanfa sun qunsa bakin ciki a zuciyar wannan 'ya tasu, sekaga wata dalilin haka ta fada ga zinace zinace, wata sekaga ta kangarema iyayen bata musu biyayya kokuma ta auka ma shan miyagun qwayoyi kokuma ta auka cikin wannan bala'in na madigo wanda yazama fitina ga musulmai ahalin yanzu****_
          _To lallai 'yan uwa daga cikin hanyoyinda zamubi mu yaqi matsalar zinace zinace da madigo acikin wannan al'umar tamu, shine aduk sadda mutumin kirki bawan Allah me addini da kyawawan dabi'u yafito neman auren 'yarmu to lallai mubashi kada tunanin wani abin duniya wanda ba me dorewa ba, yasa muhanashi bayan kuma shi yanason yarinyar itama tana sonshi****_
=
=
Zamu dakata anan sekuma bayani nagaba idan Allah yakaimu
=
_Almajirinku ne kamar kullun, dan mutanen Kabo_
.
```Jameel Alhassan Haruna kabo```
.
_(Alwahhaby, Assalafy)_
.
.
Allah ta,ala yasa mudace.mahuta.com.ng

No comments:

Post a Comment

Yadda zaka samu Maki 280 a jamb

Assalamu Alaikum, wadannan shawarwarine da babu shakka idan dalibi ya bisu sau da kafa to Insha Allahu zai samu gagarumin maki a jaraba...