Adthis

Yadda Zaka Goge Bashin Dakaci A Kowani Layin MTN Batareda Kosisin Ka Ba

Tuesday, 15 January 2019

Yadda Zaka Nemi Aikin Zabe(Ad-hoc Staff)

Yadda Zaka Nemi Aikin Zabe Na 2019.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta saki form na neman aikin zaben shekara 2019.

Neman aikin yakasu zuwa biyu:
• Ma’aikatan wucin Gadi (Adhoc Staff – RATECH)
• Ma’aikatan INEC na dindin din (LGATECH)

Ana iya rijistar wannan ayyuka guda biyu a shafin INEC na yanar gizo wato pres.inecnigeria.org Sai dai kuma ba kowa zai ci gajiyar aikin ba, har sai mutun ya cika ka’idojin da sashen fasaha na hukumar zaben ya gindaya.

Sharudan Rijista Dan Zama Adhoc Staff – RATECH
Mutane Kala uku ne za su iya rijistar wannan aikin.
1. Wanda ya yi bautar kasa da hukumar INEC tsakanin 2013 zuwa 2018 (Ex-coper)
2. Ma’aikacin hukumar INEC mai Karamar diploma zuwa sama. Ya zamana yana da ilimin na’ura mai kwaqwalwa.
3. Dalibin jami’ar tarayya ko kwaleji ko poly wanda saura shekara daya ya gama karatu. Shi ma sai yana da ilimin na’ura mai kwakwalwa.

Abubuwan Da zaka tanada
• Dole ne ya zama kana da lambar waya da kuma email address
• Referral letter daga ma’aikacin gwamnati da ya taka matsayin aiki na GL14 zuwa sama.
• Hoton ID card.

Sharudan Rijista Dan Zama INEC Staff – LGATECH
• Iya ma’aikacin INEC mai ordinary national diploma zuwa sama zai iya register. Shi ma sai yana da ilimin na’ura mai kwakwalwa.
• Dole ne ya zama kana da lambar waya da kuma email address
• Hoton ID card.

No comments:

Post a Comment

Yadda zaka samu Maki 280 a jamb

Assalamu Alaikum, wadannan shawarwarine da babu shakka idan dalibi ya bisu sau da kafa to Insha Allahu zai samu gagarumin maki a jaraba...