Adthis

Yadda Zaka Goge Bashin Dakaci A Kowani Layin MTN Batareda Kosisin Ka Ba

Friday, 15 March 2019

Dalilan Da Suke Sa Yan Matan Jami'a Wahalar Samun Mazan Aure1) Ta samu gurbin ci gaba da karatu a wata jamia, mahaifanta
sun yarda da ita da tarbiyyar da suka ba ta sai suka amince ta
tafi saboda abun da ta ke so kenan ci gaba da karatu. Saurayin
da yake son ta shi ma ya ce ba komai zai jira ta.
2) Da ta tsinci kan ta a bakon muhallin da take ta muradin
zuwa, ta hadu da sabbin mutane amma dai wadanda suka fi
jan hankalinta sune irin wadanda ake kira da manyan yara,
masu kai da gashi a cukurkude kamar shekar ungulu da sa
wanduna masu zama a rabin mazaunai kamar suna jin kashi,
ga mota kuma duk wayoyinsu iPhone ne latest. Ita ma saboda
kyan ta kuma saboda su mayun fararen mata ne ta ja
hankalinsu.
3) Lokaci ya tafi a yayin da alakarta da manyan yara ta fara
nisa, suna kashe mata kudi fiye da yadda ake ba ta a gidansu,
a hankali sai ta yi watsi da wannan yardar ta mahaifanta, ta
watsar da komai a yayin da yaudarar manyan yara ta rinjaye ta
ta fara baza musu kafa.
4) Saurayinta na gida ya fara korafin ta daina daga wayarsa,
abun da bai sani ba shine saboda yanzu tana rayuwa da
manyan yara masu gashi ta fara ganinsa wani local, da wani
sunansa Garba kamar garmar noma da kansa marar gashi
kamar kabewa. Daga baya dai ya ga ba zai iya jura ba, ita ma
kuma ta sanar masa ya hakura da ita ya nemi wata a
makwabta daidai shi.
5) Lokaci yana ta tafiya har an yi shekara guda an dauki sabbin
dalibai, shekar manyan yara ta fara tashi daga kan ta zuwa kan
sabbin dauka, ta neme su a waya da kuma a aji amma sun ki
saurararta.
6) Da daddare ta kasa barci saboda tunane-tunane, ta janyo
wayarta ta shigo facebook akalla ko za ta ga wani abu da zai
debe mata kewa amma ba ta gani ba sai wanda yake shirin
rusa mata kwakwalwa, saurayinta da ya ce zai jira ta ita kuma
ta ce ya bar ta, ya bar ta din da dadewa kuma gashi yanzu ya
dora katin daurin aurensa. Ta ji kamar duniyarta an dawo da ita
sama na kallon kasa.
7) Ta kashe duk kudadadenta kuma in ta nema a gida sai ta yi
awanni na bayanin abun da ta yi da su kafin ta samu wani,
manyan yara sun koma da shekarsu kan wasu, abincinta ya
kare. Tana ta tunanin neman mafita kafin a karshe ta yanke
shawarar ta kira tsohon saurayinta.
8) Ta kira shi ta ba shi hakuri, ya sanar mata komai ya wuce
amma dai lokaci ya kure. Ta nemi ya taimaka ya ara mata kudi
ko 3K ne, ya ce ba komai zai turo mata 5K kyauta, kuma bai
kullace ta ba , za ma su iya zama abokai.
9) Ta yi kuka kamar ba gobe musamman ma lokacin da ta hau
whatsApp ta duba status ta ga tsohon saurayinta ya dora
hotonsa da wacce zai aura, ta ji kamar ta tura masa da emoji
na miciji saboda tsabar yadda ta ji ta tsane ta, amma dai ba ta
yi ba.
10) Bayan kwanaki da aladarta ta yi latti da kwana hudu da
wasu bakin alamu, hankalinta ba karamin tashi ya yi ba, ta
yanke shawarar ta yi pregnancy test. Ta siyo kit din, ta zo ta
shirya komai ta tsaya tana kallon kit din a cikin tsananin
damwua tana adduar kar layuka biyu su bayyana.
A karshe layuka biyun sun bayyana, ya bayyana tana da ciki. Ta
yi nadama matsananciya, ta butulcewa yardar mahaifanta a
kanta, ta bi son zuciyarta. Ta yi ihu, ta cukurkuda gashin kanta,
ta daki gado kafin ta ji kamar ta kashe kanta.
Amma kuma kashe kai baya maganin damuwa ko ciwo, hasali
ma dai damuwar ake rabawa dangi da masoya muddin rai!
Abubakar Auyo

No comments:

Post a Comment

Yadda zaka samu Maki 280 a jamb

Assalamu Alaikum, wadannan shawarwarine da babu shakka idan dalibi ya bisu sau da kafa to Insha Allahu zai samu gagarumin maki a jaraba...