Adthis

Yadda Zaka Goge Bashin Dakaci A Kowani Layin MTN Batareda Kosisin Ka Ba

Saturday, 6 April 2019

Yadda zaka samu Maki 280 a jambAssalamu Alaikum, wadannan shawarwarine da babu shakka idan dalibi ya bisu sau da kafa to Insha Allahu zai samu gagarumin maki a jarabawarsa ta Jamb.

Kamar yadda dalibai suka sani an fara fitar da slip na jamb wato takardar dake dauke da rana da wurin yin jarabawar, wadannan shawarwarin za su taimaka matukar wajen samun gagarumar nasara


1. Ka tabbatar ka karanta littafin da Jamb suke bayarwa sosai da sosai, inda baka gane ba kayi tambaya, kada ka tsallake wuri wai don baka sani ba.
2. Ka tabbatar kayi Register akan lokaci, wannan zai baka dama kayi jarabawarka akan lokaci, sannan wajen register kayi nazari sosai kar ka cike ko aciki maka abinda bashi kake bukata ba.
3. Ka duba syllabus da suka baku na wuraren da za’a yi muku tambayoyi akai ka tabbatar ka bibiyesu sosai da sosai.
4. Ka tsara time table din karatu lokaci kaza zaka yi kaza lokaci kaza zaka yi kaza.
5. Ka tabbatar kana da sanayya akan computer musamman bangaren yadda ake zana jarabawa, idan baka sani ba ka nemi littafi na mai suna “Takardar Sanin Makama Ga Daliban Da Zasu Zana Jarabawar Jamb”

No comments:

Post a Comment

Yadda zaka samu Maki 280 a jamb

Assalamu Alaikum, wadannan shawarwarine da babu shakka idan dalibi ya bisu sau da kafa to Insha Allahu zai samu gagarumin maki a jaraba...